Hukumar Hisbah ta wajabta kwasa-kwasai kan zamantakewar aure ga masoya gabanin aure

Hukumar Hisbah ta wajabta kwasa-kwasai kan zamantakewar aure ga masoya gabanin aure

  • Hukumar Hisbah ta ce dole masoya su halarci kwas kan zaman aure kafin a daura aurensu
  • Sannan sai ma’auratan sun je an musu gwaje-gwajen lafiyarsu kafin a daura musu aure
  • Hisbah ta ce matakin ya zama dole sakamakon karuwar mace-macen aure a jihar

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta ce daga yanzu za ta bukaci dukkanin masoyan da suke shirin aure mabiya addinin Musulunci a jihar da lallai sai sun halarci kwasa-kwasai kan zamantakewar aure domin tabbatar da sun cancanci auren kafin a daura musu aure.

Babban Kwamandan hukumar Harun Ibn-Sina, ya fada a ranar Alhamis cewa bijiro da wannan tsarin ya zama wajibi lura da yawaitar matsalolin muruwar aure tsakanin ma’aurata a jihar, rahoton SR.

Ya kuma nunar da cewa dole ne sai masoyan da ke shirin auren sun je asibiti an tabbatar da lafiyarsu.

Kwamandan yace:

"Hukumar na iya kokarinta wajen ganin an samu raguwar mace-macen aure inda take wayar wa da ma’aurata kai yadda za su nuna wa juna soyayya da kauna tare da fahimtar juna a tsakaninsu.
“Galibin matan da ake sakin nasu, masu kananan shekaru ne da suka haifi ‘ya’ya hudu zuwa biyar inda ake barin su wajen kulawa da nauyin ‘ya’yansu,”

Ya ce hukumar ta dauki matakin ne lura da yadda matsalolin zamantakewar aure da ake gabatar wa gaban hukumar suke ta hauhawa kullum.

Kwamandan kara da cewa yace:

“Mace-macen aure sun sanya yara da dama kulla abokantaka da miyagun abokai da ke sanya su shiga aikata danyen aiki.
“Akwai bukatar ma’aurata su nuna wa juna soyayya da kauna da ma samun fahimtar juna tsakaninsu."

DUBA NAN: Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 na Gwamna Zulum

Hukumar Hisbah ta wajabta kwasa-kwasai kan zamantakewar aure ga masoya gabanin aure
Hukumar Hisbah ta wajabta kwasa-kwasai kan zamantakewar aure ga masoya gabanin aure

KU KARANTA: Amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen barazanar tsaro ba, Jami’in Soja

Ya kuma bukaci malaman addini da iyaye da su ja hankalin ‘ya’yan nasu kan muhimmancin zaman lafiya a ibadar aure.

Ya kamata mata su rika juriya a gidan Aure

A nata bangaren, mataimakiyar babban kwamandan mai lura da sha’anin mata da aure, Hafsat Waziri, ta ce akwai bukatar iyaye mata su rika yawaita addu’o’i tare da nuna juriya a zamantakewar aurensu.

Tace:

“Aure ba yana nufin zaman farin ciki na kullum ba, akwai bukatar mata da miji su zama masu tallafa wa juna.
“Yawaitar yadda ake sakin mata a halin yanzu abin akwai tashin hankali ciki. Don haka, ya kamata ma’aurata su zage damtse wajen ganin sun ci gaba da zaman tare."

Asali: Legit.ng

Online view pixel