Tsohon Shugaban NHIS: Gumi Ya Zargi Tinubu da Kama 'Yan Adawa da Manufar Siyasa

Tsohon Shugaban NHIS: Gumi Ya Zargi Tinubu da Kama 'Yan Adawa da Manufar Siyasa

  • Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargadi shugaba Bola Tinubu kan kama ‘yan adawa, ana zarginsa da ramuwar gayya
  • Malamin ya ce kama tsohon Shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf, yana nuna zalunci a lokacin da ƙasa ke fama da matsalolin tattalin arziki da siyasa
  • Hukumar EFCC ta cafke Farfesa Usman Yusuf a gidansa da ke Abuja bisa zargin aikata almundahana da kudin gwamnati da suka kai N4bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi gargadi ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan kama mutanen da ke sukar gwamnatinsa.

Malamin ya yi zargin cewa kama tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf, wani abu ne da ke nuna zalunci da kuma ramuwar gayya ta siyasa.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban NHIS, Usman Yusuf ya shiga matsala, EFCC ta kutsa gidansa a Abuja

Gumii
Sheikh Gumi ya kalubalanci Tinubu kan kama tsohon shugaban NHIS. Hoto: Bayo Onanuga| Salisu Web Master
Asali: Twitter

Legit ta tattaro kalaman Sheikh Ahmad Gumi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumi: “Kama Farfesa Yusuf zalunci ne”

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa kama Farfesa Yusuf a irin wannan lokaci na matsin tattalin arziki da rudanin siyasa ba abu ne mai kyau ba.

Malamin ya ce irin waɗannan matakai na iya shafar martabar gwamnatin Tinubu a idon 'yan Najeriya.

A Sheikh Gumi:

"An cafke mutane bisa tuhuma da ke nuna ramuwar gayya ta siyasa, hakan ba abu ne mai kyau ba a irin wannan lokaci da Najeriya ke fama da matsaloli."

Sheikh Gumi ya kara da cewa ya san Farfesa Yusuf sama da shekaru 49, kuma ya tabbatar da cewa mutumin kirki ne da ke adawa da duk wani nau'in zalunci tun zamanin su na jami’a.

Kara karanta wannan

Yaki da talauci: Gwamnan Jigawa ya raba tallafin kudi ta katin ATM

A kan haka malamin ya bukaci shugaba Tinubu da kada ya bari 'yan-miya-ta-yi-dadi su bata masa suna.

Dalilin kama Farfesa Yusuf Usman

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC sun dira gidan tsohon Shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf, da ke Abuja da misalin karfe 4:30 na yamma a ranar Laraba, inda suka kama shi.

Majiyoyi daga hukumar EFCC sun tabbatar da cewa Farfesa Yusuf yana hannun hukumar, kuma ana yi masa tambayoyi kan badakalar wasu makudan kudi.

Premium Times ta rahoto cewa ana zargin ya tafka almundahana a fannin fasahar zamani, aka ce ya kara kasafin kudi daga N4.9bn zuwa N8.7bn ba tare da bin ka’ida ba.

Karin zargin da ake yi wa Farfesa Yusuf Usman

Majiyoyin EFCC sun bayyana cewa ana binciken Farfesa Yusuf bisa zargin amfani da mukaminsa wajen amfanar da kansa da kuma bayar da kwangiloli ba tare da bin doka ba.

Kara karanta wannan

Jerin ma'aikatun da wuraren da aka sanya wa sunan Bola Tinubu bayan hawansa mulki

Rahotanni sun nuna cewa binciken kan zarge-zargen da ake masa ya samo asali ne daga wata takardar korafi da aka shigar tun ranar 31 ga Oktoba, 2018.

A cewar takardar korafin, ana zargin Prof. Yusuf da aikata ayyukan rashawa da nuna babakere a lokacin da yake shugabancin NHIS.

Ce-ce-ku-ce kan kama tsohon shugaban NHIS

Kama Farfesa Yusuf ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma. Wasu na ganin abin da ake masa ramuwar gayya ce ta siyasa, yayin da wasu ke ganin ya dace a bincike shi idan akwai hujja.

Yanzu haka, ana ci gaba da sauraron matakin da gwamnati da EFCC za su dauka kan lamarin, yayin da magoya bayansa da sauran ‘yan Najeriya ke sa ido kan yadda za a kare.

An sanyawa ma'aikatu 4 sunan Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanyawa wasu ma'aikatu sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga hawansa mulki.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan kasa inda wasu ke ganin hakan bai dace ba yayin da wasu ke ganin babu matsala a matakin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel