Badakalar N110bn: Shaidun EFCC Sun Kada Hantar Lauyan Tsohon Gwamna, Yahaya Bello
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT Abuja - Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya ta dage sauraron shari’ar zargin almundahana da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, zuwa ranar 3 Afrilu da 6 Mayu, 2024.
Mai shari’a Maryann Anenih ce ta dage shari’ar domin ci gaba da sauraron shaidu bayan an kira shaidar farko, Fabian Nworah, wanda ke harkar gine-gine, don bayar da shaida.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce yayin da aka kira shari’ar domin ci gaba da sauraro, lauyan masu gabatar da kara, Kemi Pinheiro (SAN), ya shaidawa kotu cewa yana da shaidu guda biyar.
Sai dai Mai shari’a Anenih ta bayyana cewa ba za ta iya sauraron fiye da shaida guda ba, duba da cunkoson ayyukan da ke gabanta, saboda haka ga dage zaman zuwa Afrilu.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin badakala: Kotu ta soke zaman Alhamis
Channels TV ta ruwaito cewa kotun ta kuma sanar da cewa ba za ta zauna a ranar Alhamis kamar yadda aka tsara ba bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba, bayan maganar yawan aiki.
A yayin zaman, lauyan wadanda ake kara na farko da na biyu, Joseph Daudu (SAN), ya sanar da kotu cewa masu shigar da kara ba su mika masu bayanan shaidun EFCC ba.
Lauyoyin wadanda ake kara sun yi korafi
Joseph Daudu (SAN) ya ce har yanzu wanda ake kara na farko bai yi wani jawabi a kan zargin da ake yi wa wanda ya ke wakilta a gaban kotu ba.
Ya ce;
“Ba a mika mana bayanan wanda ake kara na biyu ba, domin mu tantance ko muna da ikon kare shi yadda ya dace ko a’a ba.
“Wannan babban cikas ne a gare mu. Dole ne a ba mu duk bayanan da wadanda ake kara suka bayar.

Kara karanta wannan
Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su
“Gaskiya na fahimci wanda ake kara na farko bai bayar da wani bayani ba tukuna. Amma dai har yanzu muna cikin matakin shiryawa don fara shari’a.”
Lauyan EFCC ya musanta zargin takaita bayanai
A nasa bangaren, lauyan masu gabatar da kara, Kemi Pinheiro (SAN), ya musanta zargin lauyoyin wadanda ake kara, yana mai cewa suna kokarin jinkirta shari’ar.
Ya ce:
“Dokar da suke dogara da ita ba ta nufin cewa dole ne masu gabatar da kara su mika dukkan takardu da suke da su.
“Dokar ta ce kawai a mika wa masu karewa takardun da suka bukata,” in ji Pinheiro.
EFCC: Yahaya Bello ya fito daga kurkuku
A wani labarin, kun ji cewa a daren Juma'a, 20 Disamba 2025 ne tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya shaki iskar 'yanci bayan cika dukan sharudan beli da kotu to gindaya.
An saki Yahaya Bello ne daga gidan yarin Kuje bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, ta bayar da belinsa kan kuɗi N500m tare da gabatar da mutum uku da za su tsaya masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng