Kudiri Yayi Nisa a Majalisa, Gwamna Abba Zai Kafa Hukumar Tsaro Mallakin Jihar Kano

Kudiri Yayi Nisa a Majalisa, Gwamna Abba Zai Kafa Hukumar Tsaro Mallakin Jihar Kano

  • Majalisar Dokokin Kano ta yi karatu na biyu a kan kudirin kafa Hukumar Tsaro ta Jihar Kano don tallafawa jami’an tsaro
  • A zaman majalisar na ranar Talata, an bayyana cewa ana sa ran bai wa hukumar ikon rike makami da tsare wanda ake zargi da laifi
  • ‘Yan majalisa sun nuna damuwa kan yawaitar kwacen wayoyi, ayyukan ‘yan daba da safarar miyagun kwayoyi a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kudurin dokar kafa hukumar tsaro ya tsallake karatu na biyu a zaman Majalisar dokokin jihar Kano da ya gudana a ranar Talata.

‘Yan majalisa masu wakiltar mazabun Nassarawa da Kiru, Hon. Yusuf Aliyu da Hon. Usman Tasiu ne su ka gabatar da kudirin a gaban majalisa da zummar inganta tsaro.

Kara karanta wannan

"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe

Assembly
Ana shirin samar da hukumar tsaro mallakin jihar Kano Hoto: Honorable Spealer Kano State House of Assembly
Asali: Facebook

Leadership News ta wallafa cewa ‘yan majalisa masu gabatar da kudirin sun ce manufar dokar ita ce karfafa tsaro a karkashin hukumar da za ta karbi umarni daga Gwamna kai tsaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun jaddada cewa wannan hukuma za ta taimaka wa Jihar Kano wajen tallafawa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya domin tabbatar da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Majalisa ta amince a samar da hukumar tsaro

Daily Post ta ruwaito ta wallafa cewa dan majalisa, Hon. Lawan Husseini, wanda shi ne shugaban masu rinjaye, ya jagoranci karatu na biyu na kudirin dokar yayin zaman da Kakakin Majalisar, Hon. Isma’il Falgore, ya jagoranta.

Bayan zaman, Hon. Husseini ya yi wa manema labarai karin haske a kan kudirin, yana mai bayyana abin da hukumar za ta yi idan an kafa ta.

Ya nanata cewa za ta kasance mai bayar da tsaro ga al’ummar Kano tare da taimaka wa jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da doka a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gamu da matsala: Kotun Kano ta yi hukunci kan kama Muhuyi Magaji

'Yan Majalisa sun damu da matsalar tsaro

Hon. Lawan Husseini ya bayyana cewa akwai karuwar matsalar tsaro a wasu yankuna na Kano da ke bukatar karin jami’ai domin dakile ayyukan bata gari.

Ya ce:

“Kamar yadda kowa ya sani, matsalolin rashin tsaro sun karu a Kano, tun daga kwacen wayoyi, ayyukan ‘yan daba, har zuwa safarar miyagun kwayoyi.
"Idan aka kafa wannan hukuma, za ta taka muhimmiyar rawa wajen rage wadannan laifuffuka a jihar.”

“Hukumar za ta iya kame,” Majalisar Kano

Shugaban masu rinjaye, Hon. Lawan Husseini, ya bayyana irin karfin ikon da ake fatan bai wa sabuwar Hukumar Tsaro da ake fatan samarwa a Jihar Kano.

Ya ce hukumar za ta samu damar rike makamai, yin kame, tare da mika wadanda ake zargi ga ‘yan sanda domin gurfanar da su a gaban kotu.

Hon. Dala ya bayyana cewa za a nada kwamanda-janar da zai jagoranci ayyukan hukumar, tare da kwamitin gudanarwa da ke kunshe da mutanen da suka cancanta, ba tare da tasirin siyasa ba.

Kara karanta wannan

Wani katafaren otal da kamfanoni 4 sun shiga gonar gwamnatin Kano, an ɗauki mataki

Gwamnan Kano ya yi nade-naden mukamai

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da wasu muhimman nade-naden mutane hudu domin tafiyar da gwamnatin jihar Kano.

A sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya ce wadannan nade-nade sun yi daidai da aniyar gwamnatin Abba Kabir Yusuf na aiki da kwararru masu hazaka domin ci gaban Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel