Kano: Abba Gida Gida Ya Jawo Hadimin Kwankwaso, Ya Nada Shi a Mukami
- Gwamnan jihar Kano ya nada Ibrahim Adam, wanda ya kasance tsohon hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin tallafa wa tawagar labaransa
- Ibrahim Adam yana daga cikin matasa masu tasiri wajen tallata nasarorin gwamnatin jihar Kano, kuma ya taba zama hadimin Abba a lokacin takara
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya sabon hadimin nasa murna tare da jan hankalinsa kan mahimmancin jajircewa da bayar da ingantattun bayanai ga jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Ibrahim Adam, tsohon hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a cikin tawagar yada labaransa.
An ba Ibrahim mukamin domin yin aiki a matsayin Mai Bai wa Gwamnati Shawara Kan Harkokin Labarai na tawagar Abba Kabir Yusuf.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sanarwar nadin ta fito ne daga bakin Darakta Janar na yada labaran gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene sabon hadimin gwamnan Kano?
Ibrahim Adam, mai shekaru 32, ya kammala karatun digiri a fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Bayero da ke jihar Kano.
Shi ne ɗaya daga cikin fitattun masu tasiri a kafafen sada zumunta, waɗanda suka taka rawar gani wajen tallata nasarorin wannan gwamnatin.
A baya, ya yi aiki a matsayin Mataimaki na Musamman ga Abba Kabir Yusuf lokacin da yake takarar gwamna a tsakanin shekarun 2020 zuwa 2022.
Yadda Ibrahim ya zama hadimin Kwankwaso
Bayan rawar da Ibrahim Adam ya taka a lokacin takarar Abba Kabir Yusuf, sai aka nada shi a matsayin Mataimaki na Musamman ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya riƙe wannan mukamin har zuwa nadin da aka yi masa a matsayin Mai Bai wa Gwamnati Shawara Kan Harkokin Labarai.
Gwamnan Kano ya shawarci sabon hadiminsa
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya sabon hadimin nasa murna tare da ba shi shawarar da ya nuna kwarewa, jajircewa, da aiki tare da sauran mambobin gwamnati.
Haka kuma, gwamnan ya yi kira ga Ibrahim Adam da ya ba da cikakkiyar gudunmawa wajen samar da ingantattun bayanai kan manufofi da shirye-shiryen wannan gwamnati.
Gwamnan ya bayyana gamsuwa da jajircewa sabon hadimin, wanda ya zama jigo a wajen zabensa da ba shi sabon mukamin a gwamnatin jihar Kano domin yada ayyukanta.
Gwamnatin Kano ta yi wa matasa afuwa
A baya, mun ruwaito cewa Antoni Janar na Kano, Haruna Dederi, ya bayar da umarnin dakatar da dukkan shari’o’in laifuka da ake yi wa masu zanga-zangar #EndBadGovernance a jihar Kano.
Matakin ya biyo bayan koke da kungiyar Citizens’ Gavel ta gabatar ta na neman a kawo ƙarshen tuhumar matasan da suka fito kan tituna domin nuna adawa da manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
Matasan Najeriya sun fito daga ranar 1 zuwa 10 Agusta, 2024, suna adawa da yadda ake gudanar da mulkin gwamnati a karkashin Bola Tinubu, wanda su ke zargin ya na ta'azzara matsalolin kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng