Gwamnatin Kano Ta Yafewa Masu Zanga Zanga, An Dakatar da Shari'ar Zargin Cin Amanar Kasa

Gwamnatin Kano Ta Yafewa Masu Zanga Zanga, An Dakatar da Shari'ar Zargin Cin Amanar Kasa

  • Antoni Janar na jihar Kano, Haruna Dederi, ya ba da umarnin dakatar da dukkan shari’o’in laifuka da ake yi wa masu zanga-zanga
  • Daga ranar daya zuwa 10 Agusta, 2024 ne wasu daga cikin matasan Najeriya su ka fito tituna domin adawa da manufofin Bola Tinubu
  • Ana zargin masu zanga-zangar da taro ba tare da izini ba da tayar da hankula, amma a yanzu gwamnatin Kano tajanye tuhume-tuhumen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - A ranar 27 ga Janairu, 2025, Antoni Janar na Kano, Haruna Dederi, ya ba da umarnin dakatar da dukkan shari’o’in laifuka da ake yi wa masu zanga-zangar #EndBadGovernance a jihar.

Wannan matakin ya biyo bayan koke da kungiyar Citizens’ Gavel ta gabatar a ranar 5 ga Nuwamba, 2024, ta na neman a kawo karshen tuhumar da ake yi wa matasan.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Kabir
Gwamnatin Kano ta janye shari'a da wanda su ka yi zanga-zanga Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Leadership News ta bayyana cewa Antoni Janar ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki na 1999, sashi na 211(1)(c), ya ba shi domin kawo ƙarshen tuhume-tuhumen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da alama gwamnatin Kano ta amsa koken, inda Antoni Janar din ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano ta janye dukkanin zargin da ake yi wa matasan.

An jinjina wa matakin gwamnatin Kano

Kungiyar Citizens’ Gavel ta yaba wa matakin gwamnatin jihar Kano na dakatar da shari’o’in da ake yi da masu zanga-zangar adawa da yunwa.

Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin babban ci gaba wajen tabbatar da adalci da ‘yancin ɗan Adam a Najeriya.

“Gwamnatin Kano ta mutunta jama’a.” Kungiya

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Rachael Adio, ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa wannan mataki yana nuna jajircewar Antoni Janar na Kano wajen mutunta dokokin ƙasa da ‘yancin al’umma.

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

“Wannan matakin na dakatar da shari’o’in ya nuna jajircewar gwamnatin jihar Kano wajen mutunta ‘yancin walwala da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar wa ‘yan ƙasa.”

Kano: Zargin da aka yi wa masu zanga-zanga

Masu zanga-zangar sun fuskanci zarge-zarge da suka haɗa da haɗa baki don tayar da husuma da cin amanar ƙasa, taro ba tare da izini ba, da kuma tayar da hankali a bainar jama’a.

Sai dai kungiyar Citizens’ Gavel ta ce zarge-zargen ba su da tushe ballantana makama, ganin dalilan da su ka sa jama’a fitowa zanga-zangar.

Kungiyar ta bayyana matakin Antoni Janar na Kano a matsayin wanda ya dace kuma yana ƙarfafa fata kan bin doka da oda a Najeriya.

Gwamnatin Kano ta amsa koken jama’a

Kungiyar ta jinjina wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf kan sauraron koke da al’umma suka gabatar a kan makomar masu zanga-zangar.

Ta ce wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci wajen nuna shugabanci na gari da kuma kare walwala da haƙƙin al’umma.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su

Gwamnan Kano ya yi nade-nade

A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano ta sanar da nade-naden sabbin kwararru a muhimman mukamai domin cimma muradunta na inganta ci gaba a jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Jamila Magaji Abdullahi a matsayin sabuwar Akanta Janar ta jiha, da Injiniya Abubakar Sadiq a matsayin Mataimakin Darakta Janar na RUWASA.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.