'Annabi Ya Fadi Amfanin Namansu ga Lafiya': Abba Kabir Ya Kare Matakin Raba Awaki a Kano
- Gwamna Abba Yusuf ya kare shirin bayar da awaki ga mata, yana cewa naman awaki na da amfani sosai wajen magance cututtuka da bunkasa tattalin arziki
- A karkashin shirin, an raba awaki 7,158 ga mata a kananan hukumomi 44 na Kano, domin rage talauci da tallafa wa mata
- Gwamnan ya ce shirin ya samu tallafi daga Bankin Musulunci, inda aka kashe Naira biliyan 2.3 don saya da rarraba awaki ga mata a jihar Kano
- Wannan ya biyo bayan suka da gwamnatin Abba Kabir ta sha kan shirin da ake ganin zamanin raba awaki ya wuce kan bunƙasa tattalin arziki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya sake yin magana kan shirin raba awaki domin tallafawa mata da kuma bunkasa tattalin arziki.
Gwamnan ya bayyana muhimmancin shirin bayar da awaki ga mata, yana cewa shirin na rage talauci da bunkasa tattalin arzikin mata.
An caccaki Abba Kabir kan raba awaki
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa shi ya tabbatar da aka a cikin wata sanarwa da Daily Nigerian ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar cewa gwamnan ya sha suka bayan raba awaki 7,158 ga mata a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Wannan ya kasance wani bangare na shirin rage talauci da habaka tattalin arzikin mata a jihar.
Gwamnatin Abba ta kare matakin raba awaki
Yayin kare shirin, gwamnan ya ce shirin ya ci Naira biliyan 2.3, gwamnan ya ce naman awaki na da amfani sosai ga lafiyar jikin dan Adam.
Dawakin-Tofa ya ce wannan tsari shi ne mataki na biyu na shirin habaka tattalin arzikin mata karkashin Kano Agro-Pastoral Development Project.
"Wasu suna ganin kiwon kaji da awaki bai dace ba, amma Annabinmu (SAW) ya yi kiwon awaki, kuma ya ambaci amfanin naman awaki."
"Ina son ganin irin wannan cigaba a jihar Kano, amma wasu suna sukar wannan kokari," gwamnan ya jaddada."
- Abba Kabir Yusuf
Yadda bankin Musulunci ya ba da tallafi
Ya bayyana cewa shirin ya samu tallafi daga Bankin Musulunci, inda aka yi amfani da kudaden wajen saya da rarraba awaki ga mata.
Gwamna Abba Kabir ya bayar da misalin wata mata daga Jihar Jigawa wadda ta samu arziƙi daga kiwon awaki uku da aka ba ta a baya.
Yanzu haka, gwamnan ya ce, wannan matar tana ba da bashi ga ma’aikatan gwamnati, tana kula da iyalinta, kuma tana biya wa yara kudin makaranta.
An soki Abba Kabir kan raba awaki
Kun ji cewa fitaccen dan jarida, Jafar Jafar ya bayyana rashin jin daɗinsa kan tsarin raba awaki da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Gwamnan jihar Kano ya raba awaki akalla sama da 7,000 ga mata a Kano domin ba su damar yin kiwo domin magance talauci.
Jafar ya yi kira da a mayar da hankali kan ayyuka na zamani, yana mai nuna cewa rabon dabbobi a karni na 21 bai dace da tsarin mulki ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng