"Za Mu Gyara Inda Ya Kamata": Shettima Ya Lissafa Muhimman Ayyukan Gwamnatin Tinubu
- Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya tabbatar da cewa gwamnatin APC na yaki da cin hanci da gyara tattalin arziki
- A taron da aka gudanar a Abuja, Shettima ya ce dimokuradiyya ba cikakkiyar tsarin mulki ba ce, amma ta fi kowanne tsari inganci
- Shettima ya roki ‘yan Najeriya su goyi bayan gwamnati wajen inganta dimokuradiyya da tsayayyen tsarin mulki domin ci gaban kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya tabbatar da kudurin gwamnatin jam’iyyar APC na yaki da cin hanci da rashawa.
Kashim Shettima ya ce daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu ta sanya a gaba akwai gyaran tattalin arziki, da karfafa zaman lafiya.

Asali: Twitter
Shettima ya yi magana kan dimokuradiyya
Shettima ya bayyana wannan ne a taron kasa na karfafa dimokuradiyya a Najeriya da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, 27 ga Janairu, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron wanda mai taken: “Karfafa dimokuradiyya a Najeriya: Hanyoyin kai wa ga kyakkyawar gwamnati da karfafa siyasa,” an shirya shi ne karkashin cibiyar ACLSD.
Da ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, Shettima ya bayyana cewa dimokuradiyya ba cikakkiyar tsarin mulki ba ce.
Sai dai Shettima ya ce duk da haka, idan aka kwatanta da sauran tsare-tsaren mulki, dimokuradiyya ce mafi kyau a duniya.
Shettima ya hango nasarar Najeriya a gaba
Mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da cewa:
“Za mu saurari kowane ra'ayi kuma mu gyara inda ya kamata, kuma za mu tabbatar da amana kan abubuwan da tsarin dimokuradiyya yake bukata.
"Ina da tabbacin cewa Najeriya za ta kai tudun mun tsira, za ta cimma cikakken damar ta kuma ta zama jagora a duniya."
“An ce dimokuradiyya ba cikakken tsarin mulki ba ne, amma ya fi kowanne tsari. Za mu ci gaba da kokarin gyara kasuwar tattalin arziki da sauran bangarori.”

Kara karanta wannan
'Su bar kujerunsu': Atiku ga yan siyasa da ke sauya sheka, ya fadi hanyoyin gyara dimukraɗiyya
Shettima ya lissafa ayyukan gwamnatin Tinubu
Shettima ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta mayar da hankali wajen cin gajiyar tsarin demokradiyyar ta hanyar magance matsalolin tattalin arziki da samar da tsaro.
Sauran bangarorin sun hada da yaki da rashawa da kuma gudanar da sahihin zabe, karfafa dimokuradiyyar da tsarin shari'a da ma hadin kan kasa.
Shettima ya roki ‘yan Najeriya su goyi bayan gwamnatin da ke aiki a wannan tafiya mai wahala amma mai fa'ida, yana mai cewa gwamnati tana da bukatar inganta dimokuradiyya.
Ya kara da cewa gwamnatin Bola Tinubu tana da muhimmiyar sha’awar inganta tsarin dimokuradiyya don amfanin 'yan kasar baki daya.
Shettima ya magantu kan karbar tallafin turawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana rashin yarda da dogaro da tallafin ƙasashen waje.
Sanata Kashim Shettima ya bayyana hakan a taron tattalin arziki na duniya da ake yi a Davos-Klosters, Switzerland inda ya ce bai kamata a dogara da bashin waje ba.
Mataimakin shugaban kasar ya bukaci kasashen Afirka su yi ƙoƙari wajen amfani da albarkatun da suke da su, tare da jan hankalin masu zuba jari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng