Shehu Sani Ya Fadi Wadanda Za Su Iya Hana Karin Kudi Kira da Data a Najeriya

Shehu Sani Ya Fadi Wadanda Za Su Iya Hana Karin Kudi Kira da Data a Najeriya

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya taɓo batun ƙarin kuɗin kira da data da hukumar NCC ta yi a Najeriya
  • Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa majalisar tarayya za ta yi dakatar da ƙarin kuɗin domin tana da ikon yin hakan
  • Ya yi fatan cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da takwaransa na majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, za su yi amfani da ikon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan ƙarin kuɗin kira da data ta hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta yi.

Idan ba a manta ba dai hukumar NCC ta ƙara kuɗin kira da data da kaso 50% wanda hakan ya jawo cece-kuce.

Shehu Sani ya yi magana kan karin kudin kira
Shehu Sani ya ce majalisa za ta iya hana karin kudin kira da data Hoto: @ShehuSani, @HouseNGR
Asali: Twitter

Me Shehu Sani ya ce kan ƙarin kuɗin kira?

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

A martanin da ya yi a shafinsa na X kan ƙarin kuɗin, Shehu Sani ya bayyana cewa majalisar tarayya za ta iya hana aiwatar da tsarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani ya bayyana cewa majalisar tarayya tana da ikon da za ta hana hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) da kamfanonin sadarwa daga yin ƙarin kudin kira da data.

Tsohon sanatan ya yi fatan cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da takwaransa na majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, za su yi amfani da wannan ikon da suke da shi.

Batun ƙarin kuɗin kiran dai ya jawo cece-kuce a Najeriya inda mutane da dama suka yi Allah wadai da matakin.

"Majalisar tarayya tana da ikon dakatar da NCC da kamfanonin sadarwa daga ƙara farashin kiran waya da data. Ina fatan mai girma Sanata Akpabio da Rt. Hon.Tajudeen Abbas za su yi amfani da wannan ikon."

- Shehu Sani

Ƴan Najeriya sun yi martani

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

@AbbaM_Abiyos:

"Ba na tunanin za su yi hakan, dukkaninsu ƴan amshin shatar ɓangaren zartarwa ne"

@jidifeanyi:

"Idan ba su yi ba, NLC za ta yi, idan su ma sun kasa, jama'a za su yi abin da ya dace."

@Jaaf247:

"Dama har yanzu muna da majalisar tarayya?"

@Muyiwa50138:

"Me ya sa?? Ka taɓa tsayawa ka bincika kuɗaɗen waɗannan kamfanonin suke kashewa? Albashi, kashe-kashen gudanarwa, da sauran kuɗaɗen sun ƙaru sosai, amma kana son farashi ya tsaya a inda yake."
"Ingantaccen sabis ba shi da arha a ko ina. Ka kasance mai adalci ga waɗannan kamfanonin. Suna fama da wahala."

@arubu-jr:

"Abin bai shafesu ba, ba za su dakatar ba. Mugaye kawai."

@uzidanaudu0001:

"Shin dama Akpabio ya taɓa yin wani abu mai amfani ga talaka."

@truthunleashed3:

"Shin kamfanonin sadarwa ba sa siyan man fetur ne? Ka ƙyalesu kawai."

SERAP ta maka Tinubu ƙara kan ƙarin kuɗin kira

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta shigar da gwamnatin Bola Tinubu da hukumar NCC ƙara a gaban kotu kan ƙarin kuɗin kira da data.

Kara karanta wannan

Sukar APC: Shehu Sani ya yi wa El-Rufai wankin babban bargo

Ƙungiyar SERAP a ƙasar da ta shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta buƙaci a hana NCC da kamfanonin sadarwa aiwatar da ƙarin kuɗin.

Ta bayyana cewa ƙarin ya saɓawa ƙa'ida kuma tauye haƙƙin ƴan ƙasa ne na ƴancin faɗar albarkacin bakinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng