Shugaba Tinubu Zai Sake Barin Najeriya, Wannan Karon Zai Shilla zuwa Tanzaniya
- Shugaba Bola Tinubu zai halarci taron makamashi na shugabannin Afirka, wanda zai gudana a Dar es Salaam, da ke Tanzaniya
- Taron zai mayar da hankali kan gano hanyar inganta makamashi da jawo kamfanoni masu zaman kansu don dorewar makamashi
- An ce Tinubu zai tabbatar wa shugabannin Afrika irin rawar da Najeriya ta ke takawa a bunkasar makamashi da samar da wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Lahadi zuwa birnin Dar es Salaam da ke a kasar Tanzaniya.
An ce shugaban kasar na Najeriya zai je Tanzaniya ne domin halartar taron shugabannin Afirka kan makamashi a ranar 27-28 ga Janairu, 2025.

Asali: Twitter
Tinubu zai shilla zuwa kasar Tanzaniya
Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar.

Kara karanta wannan
"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tanzania tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Raya Afirka da Bankin Duniya ne za su dauki nauyin taron, a cewar kakakin Tinubu.
Bayo Onanuga ya ce taron zai mayar da hankali kan bunkasa shirin "Mission 300," don samar wa mutane miliyan 300 wutar lantarki a Afirka zuwa shekarar 2030.
Abubuwan da za a tattauna a taron Tanzaniya
A birnin Dar es Salaam, shugabannin Afirka, shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, da kungiyoyin fararen hula za su tattauna dabarun kara samun wutar lantarki a nahiyar.
Sanarwar ta ce taron zai zama dandamali na musayar ilimi, kwarewa, da albarkatu don magance matsalolin makamashi a Afirka.
An kara da cewa tattaunawar za ta mayar da hankali kan samar da wuta a yankunan karkara, sabunta samar da makamashin, amfani da makamashi mai inganci, da jawo kamfanoni masu zaman kansu don zuba jari.
Tinubu zai yi jawabi gaban taron Tanzaniya
Wata ɓangaren sanarwar ya ce:
"A rana ta farko, kasashen da suka halarta, ciki har da Najeriya, za su gabatar da dabarunsu na cimma samar da wuta ga 'yan kasarsu cikin shekaru biyar.
"A rana ta biyu, shugabannin kasashe za su rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashi ta Dar es Salaam, wacce za ta bayyana hanyar da za a bi don cimma burin Mission 300."
Shugaba Tinubu zai yi jawabi don tabbatar da himmar Najeriya wajen samar da wutar lantarki ga kowa da rawar da kasar ke takawa wajen ci gaban makamashi a Afirka.
An lissafa wadanda za su raka Tinubu
Sanarwar ta ce Tinubu zai kuma bayyana ayyukan Najeriya na samar da makamashi mai tsafta da dabarun inganta isar da wuta a nahiyar.
Karamar ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ministan wuta, Adebayo Adelabu, da mashawarcin shugaban kasa kan makamashi, Olu Verheijen, tare da wasu manyan jami’ai za su yi wa Tinubu rakiya.

Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
Bayo Onanuga ya sanar da cewa Shugaba Tinubu zai dawo Abuja bayan kammala taron.
Mace ta zama shugabar kasar Tanzaniya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an rantsar da Samia Sulhu Hassan a matsayin shugabar kasa mace ta farko a Tanzania a ranar Juma'a, 19 ga Maris, 2021.
Ta dare kujerar shugabanci ne bayan rasuwar Shugaba John Pombe Magufuli, yayin da aka yi bikin rantsarwar a birnin Dar es Salaam.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng