Cire Tallafin Fetur: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Fadi Alherin da Najeriya Ta Samu

Cire Tallafin Fetur: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Fadi Alherin da Najeriya Ta Samu

  • Mataimakin shugaban majalisar wakilan Najeriya ya yi magana kan tagomashin da Najeriya ta samu sakamakon cire tallafin man fetur
  • Benjamin Kalu ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da gwamntin tarayya ta yi, ya yi tasiri sosai kan tattalin arziƙin ƙasar nan ta fuskoki da dama
  • Mataimakin shugaban majalisar ya nuna cewa bayan cire tallafin, gwamnati ta samu damar samun kuɗaɗe domin ɓangarorin lafiya, ilmi da sauranu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Birnin Landan - Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya ce cire tallafin man fetur ya yi tasiri mai kyau ga tattalin arziƙin Najeriya.

Benjamin Kalu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu damar adana dala biliyan 10 a shekarar 2023 sakamakon cire tallafin man fetur.

Benjamin Kalu ya yabi cire tallafin fetur
Benjamin Kalu ya ce cire tallafin fetur ya yi amfani ga Najeriya Hoto: @BenKalu
Asali: Facebook

Benjamin Kalu ya yi jawabi a Landan

Benjamin Kalu ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da wasu masu zuba jari da masana a jami’ar Oxford da ke birnin Landan, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

"Ba kamar Tinubu ba": Amaechi ya fadi yadda ya shirya samar da sauki ga talaka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da babban sakataren yaɗa labaransa, Levinus Nwabughiogu, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce mataimakin shugaban majalisar ya yi magana kan siyasa, tsaro, tattalin arziki, da ci gaban ƙasa, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Sanarwar tace mataimakin shugaban majalisar wakilan yana tare da tawagar da ta ƙunshi, Chris Nkwonta, Ginger Onwusibe da Ibe Okwara.

Me ya ce kan amfanin cire tallafin fetur?

Benjamin Kalu ya nuna cewa cire tallafin man fetur ya ba gwamnatin tarayya damar karkatar da kuɗaɗe zuwa ɓangarori masu muhimmanci kamar lafiya, ilimi, da samar da ababen more rayuwa.

Kalu wanda mamba ne na jam'iyyar APC, ya ƙara da cewa cire tallafin ya haifar da ƙarin kaso 22% cikin 100% a kudaden da ƴan Najeriya mazauna ƙetare suka turo gida, wanda ya kai jimillar dala biliyan 28 a shekarar 2024.

Har ila yau, ya bayyana cewa haɗin kai tsakanin rundunar sojojin Najeriya da takwarorinsu na sauran ƙasashen makwabta ya haifar da kama ƴan ta’adda sama da 1,500 a yankin Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Shettima ya bugi kirji a kan rashawa, ya ce za a magance matsalolin Najeriya

A ɓangaren ci gaban kasa, mataimakin shugaban majalisar ya ce gwamnati ta ƙaddamar da shirye-shirye daban-daban don inganta ci gaban fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire.

"Cire tallafin man fetur ya sanya gwamnati ta adana dala biliyan 10 a shekarar 2023, inda aka karkatar da kudaden zuwa ɓangarori kamar kiwon lafiya, ilimi, da ababen more rayuwa."
"Yayin da kuɗaɗen da ƴan Najeriya mazauna ƙetare suka turo gida suka ƙaru da kaso 22% cikin 100%, wanda ya kai jimillar dala biliyan 28."

- Benjamin Kalu

Hadimin Tinubu ya yabi cire tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin shugaban ƙasa Bola Tinubu kan hulɗa da jama'a a yakin Arewa maso Yamma, Aliyu Tanko Yakasai, ya yabi matakin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.

Hadimin na Bola Tinubu ya bayyana cewa matakin cire tallafin man fetur ɗin ya fara samarwa da ƴan Najeriya sauƙi, duk da ƴan wahalhalun da aka sha da farko.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel