Cikin Bello Turji Ya Duri Ruwa, Ya Samo Dabarar Kauce Wa Matsin Lamba daga Sojoji

Cikin Bello Turji Ya Duri Ruwa, Ya Samo Dabarar Kauce Wa Matsin Lamba daga Sojoji

  • Shugaban 'yan bindiga, Bello Turji ya yi shiru kwanan nan, bayan da aka tsananta kai hare-hare kan sansaninsa a yankin Arewa maso Yamma
  • Turji wanda ya saba amfani da bidiyo wajen nuna karfinsa, bai bayyana a bainar jama’a ba, lamarin da ya sanya tambayoyi a zukatan al'umma
  • Rahotanni sun ce Turji ya saki wasu mutanen da aka yi garkuwa da su domin rage zafin hare-haren sojoji a yankinsa
  • Hakan bai rasa nasaba da alwashin rundunar sojoji na kawo karshen ayyukan ta'addanci musamman a yankin Arewa maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - Shahararren shugaban 'yan bindiga, Bello Turji na ci gaba da shan matsin lamba daga rundunar sojoji.

Turji wanda ya yi kaurin suna wurin sakin bidiyo domin nuna karfinsa da karyata matsin lamba, ya yi shiru kwanan nan.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Hare-haren rundunar sojoji ya sake rikita dan ta'adda, Bello Turji
An gano yadda Bello Turji ya buya bayan shan matsin lamba daga rundunar sojoji. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ana zargin Turji ya tsere mahaifar Matawalle

Rahoton Zagazola Makama ya ce wannan shiru da bai saba yi ba ya tada zargin cewa ya rasa ikon tafiyar da lamura a sansaninsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa bayan zargin cewa shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, yana cikin karamar hukumar Maradun, mahaifar Bello Matawalle a jihar Zamfara yayin da sojoji suka kara matsa masa

Rahotanni sun ce an ga mabiyan Turji suna hijira a kan babura, dauke da raunana, zuwa wuraren Garsa/Kadanya a ranar 19 da 20 ga watan Janairun 2025.

An yi zargin cewa Turji yana boye tare da wasu mabiyansa a Garsa/Kadanya, tare da goyon bayan tsohon abokin gaba, Jummo Smally.

Hakan bai rasa nasaba da irin matsin lamba daga rundunar sojojin Nigeriya a yan kwanakin nan da ke neman cin masa ta kowace hanya a Zamfara.

An nemi Turji a kafofin sadarwa an rasa

Kara karanta wannan

Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin

Turji, wanda yawanci ke amfani da bidiyo don tsokanar jami'an tsaro ko kiran mabiyansa, bai bayyana ba a bainar jama’a kwanan nan.

Lamarin da da ya haifar da rade-radin cewa dan ta'addan ya shiga tsaka mai wuya ko kuma ya raunana.

Rahotanni sun nuna cewa Turji na iya fuskantar matsin lamba daga hare-haren sojoji da aka tsananta a yankinsa, musamman bayan ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ana zargin ya saki wasu mutanen don rage kai farmakin da sojoji ke yi a sansaninsa.

A halin yanzu, dakarun sojin Najeriya na ci gaba da gudanar da hare-hare kan ‘yan bindiga da matsa lamba a kan miyagun da ke addabar yankin.

Sheikh Asada ya musanta kisan ɗan Bello Turji

Kun ji cewa shahararren malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan labarin kisan ɗan Bello Turji da ake yaɗawa.

Malamin ya musanta rahoton da ke cewa an kashe dan Bello Turji inda ya ce ba gaskiya ba ne, ya ce yana raye kuma yana cikin yankin Bawa a bakin iyakar Niger.

Ya ce tun kafin farmakin da aka kai, Turji ya samu labari ya tsere da kayansa daga inda ake zaton yana nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.