Mutane Su Yi Hattara: An Gano Gurbataccen Man Ja da Ake Sayarwa a Kasuwannin Najeriya

Mutane Su Yi Hattara: An Gano Gurbataccen Man Ja da Ake Sayarwa a Kasuwannin Najeriya

  • An gano gurbataccen man ja a kasuwanni daban-daban a Najeriya, lamarin da ya jawo damuwa saboda illarsa ga lafiyar al’umma
  • Bincike ya nuna ana gurbata man ja da sinadaran rini domin kara masa yawa, wanda ke iya haifar da cutar kansa da ciwon zuciya
  • Prince Wale Oyekoya ya abbatar da cewa wasu 'yan kasuwa suna safarar gurbataccen man ja, kuma gwamnatin ta gaza dakile hakan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Masu ruwa da tsaki a kasuwar man ja da ma masu saye sun nuna damuwa game da zargin bullar gurbataccen man ja a kasuwannin kasar nan.

Bincike ya nuna cewa wannan dai ba sabuwar dabi'a ba ce, amma dai lamarin ya munana a 'yan kwanakin nan saboda talaucin da ake ciki.

Masana sun yi gargadi da aka fara sayar da gurbataccen man ja a kasuwannin Najeriya
Masana sun lissafa jihohin da ake sayar da gurbataccen man ja a Najeriya. Hoto: Osarieme Eweka
Asali: Getty Images

Rahoton jaridar Guardian ya nuna cewa wasu masu samar da man ja da dillalai sun dauki dabi'ar gurbata man ta hanyar zuba sinadaran da za su kara masa yawa.

Kara karanta wannan

Wata tankar man fetur ta sake fashewa a jihar Neja, ana fargabar mutane sun mutu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana samu bullar gubataccen man ja a Najeriya

Bincike ya nuna cewa ana karawa man ja wani sinadari da zai kara masa ja, wanda zai ja hankalin masu saye duk da cewa an gurbata shi.

Hakazalika, an gano cewa, karuwar neman da ake yiwa man ja ya sa masu gurbata man suna sayar da shi da farashi mai araha, wanda ya sa ake rububinsa.

An gano cewa farashin man ja ya karu da kashi 120% a cikin shekara daya saboda karuwar nemansa da ake yi, yayin da mutane ba su kula da gurbatacce.

Kasuwannin da ake sayar da gurbataccen man ja

Bisa ga binciken kasuwa da aka gudanar, ana sayar da galan din man ja mai cin lita biyar a kan N11,000 a yanzu sabanin N5500 da aka sayar da shi a Nuwambar 2023.

A cewar rahotonnni, gurbataccen man yanzu haka yana yawo a kasuwannin Imo, Legas, Yobe, da Filatp, yayin da yake shiga sauran jihohi a hankali.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Binciken kasuwa ya nuna cewa ana sayar da gurbataccen man ja a kasuwanni irinsu Ile-Epo, Daleko, Ikotun, Jankara, Mushin, Ajegunle, Mile 12-all da Legas.

An kuma rahoto cewa 'yan kasuwa a Ibadan, Potiskum, Jos, Abeokuta, Owerri da sauran garuruwa na cin karensu ba babbaka ba tare da la'akari da lafiyar mutane ba.

NAFDAC ta gano sinadarin rini a man ja

A 'yan kwanakin baya, hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta cafke wasu masu sayar da man ja a Potiskum da Jos bisa zarginsu da gurbata man ta hanyar zuba rini.

Kama su ya sa an gudanar da binciken man da suke sayarwa a dakin binciken hukumar NAFDAC, inda aka gano sinadari mai guba a ciki.

NAFDAC ta tabbatar da cewa man ja da aka kama na dauke da sinadaran rini, wanda ke iya haifar da kansa a jikin dan Adam.

An tona masu safarar gurbataccen man ja

Mai ba gwamnan Ogun shawara kan noma, Prince Wale Oyekoya, wanda shi ne shugaban gonar Bama ya ce shan gurbataccen man ja na da illa ga lafiya.

Kara karanta wannan

"Ban ƙwallafa rai ba": Peter Obi ya canja shawara kan kudurin zama shugaba ƙasa

Prince Wale ya ce shigo da gurbataccen man ja da rarraba shi aikin wasu masu uwa da gindin murhu ne a gwamnati kuma gwamnatin ta gaza dakatar da su.

"Gurbataccen manja na da illa ga lafiya saboda yana haifar da kansa da sauran matsalolin lafiya, kamar karin kitse da ciwon zuciya," a cewar Prince Wale.

Amfani 7 na man ja a jikin dan Adam

A wani labarin, mun ruwaito cewa likitoci na shawartar masu fama da cututtukan zuciya da su rika amfani da man ja wurin girki saboda ba shi da sinadarin kara kitse.

An kuma rahoto cewa man ja na bada matukar mamaki a bangaren kara tsayin gashi, ya na sanya cikar gashi tare da hana zubewarsa yayin da yake kara masa karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.