Tinubu Ya ba Ganduje, Gawuna Manyan Mukamai, an Jero Sauran Shugabannin Hukumomi

Tinubu Ya ba Ganduje, Gawuna Manyan Mukamai, an Jero Sauran Shugabannin Hukumomi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin shugabanni da daraktoci ga hukumomi 42 na Gwamnatin Tarayya.

Haka kuma, an yi wasu nade-naden sakatarorin hukumar tsaron farafren hula ta Civil Defence, hukumar kula da shige da fice (Immigration) da hukumar kula da gidajen yari (Prisons Service).

Ganduje
An ba Gawuna mukami Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe ne cikin sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Alhamis.

Mista Onanuga, wanda ke ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai ya bayyana cewa wanda aka ba mukaman za su fara aiki nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi sababbin nade-nade

Kara karanta wannan

Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano

Solacebase ta ruwaito cewa Shugaban kasa ya kuma nada sabon Manajan Darakta na Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya da kuma sabon Darakta-Janar na Hukumar Inganta Fasaha.

Gawuna, mutane 45 sun samu mukamin Tinubu

1. Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa, Ma'aikatar sufuri jiragen sama

Abdullahi Ganduje, Shugaban Hukumar Gudanarwa (Jihar Kano)

2. Asusun ba da lamunin gidaje na kasa (FMBN)

Nasiru Gawuna, Shugaban Hukumar Gudanarwa (Jihar Kano)

3. Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC), Ma'aikatar ci gaban matasa

Hillard Eta, Shugaban Hukuma (Jihar Cross River)

4. Cibiyar harkokin kasashen waje

Farfesa Bolaji Akinyemi, Shugaban Hukuma (Jihar Lagos)

5. Cibiyar samar da ci gaban samar da sukari

Surajudeen Ajibola, Shugaban Hukuma (Jihar Osun)

6. Kamfanin cinikin wutar lantarki na kasa

Sulaiman Argungu, Shugaban Hukuma (Jihar Kebbi)

7. Hukumar yaki da dumamar yanayi da habaka gandun daji

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya nada sabbin mukamai, an sauya wa wasu wurin aiki a Kano

Sanata Magnus Abe, Shugaban Hukuma (Jihar Rivers)

8. Cibiyar malamai ta kasa

Festus Fuanter, Shugaban Hukuma (Jihar Filato)

9. Hukumar bunkasa fasaha da sababbin kirkire-kirkire ta kasa(NBTI)

Raji Kolawole, Darakta-Janar (Jihar Oyo)

10. Cibiyar Tsare-tsare da Kula da Ilimi ta Najeriya

Victor Giadom, Shugaban Hukuma (Jihar Rivers)

11. Majalisar Rijistar Malamai ta Najeriya

Mustapha Salihu, Shugaban Hukuma (Jihar Adamawa)

12. Asusun horarwa na masana'antu

Hamma Kumo, Shugaban Hukuma (Jihar Gombe)

13. Cibiyar Fasahar Kimiyya ta Najeriya

Donatus Nwankpa, Shugaban Hukuma (Jihar Abia)

14. Cibiyar Kimiyya da Fasaha ta Sheda Complex.

Sanata Abubakar Maikafi, Shugaban Hukuma (Jihar Bauchi)

15. Ofishin Samar da Fasaha da Ci Gaban Kasa (NOTAP)

Sen. Tokunbo Afikuyomi, Chairman (Lagos State)

16. Hukumar Aika Saƙonni ta Najeriya (NIPOST)

D.J. Kekemeke, Shugaban Hukuma (Jihar Ondo)

17. Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa na Cikin Gida (NIWA)

Musa Adar, Shugaban Hukuma (Jihar Sokoto)

Kara karanta wannan

Wani katafaren otal da kamfanoni 4 sun shiga gonar gwamnatin Kano, an ɗauki mataki

18. Majalisar Karafa ta Kasa

Farfesa Abdulkarim Abubakar, Shugaban Hukuma (Jihar Nasarawa)

19. Hukumar Kula da Muhalli ta Kasa

Garba Muhammad, Shugaban Hukuma (Jihar Kaduna)

20. Hukumar Tabbatar da Tsaron Halittu ta Ƙasa (NBMA)

Mu’azu Rijau, Shugaban Hukuma (Jihar Neja)

21. Cibiyar Nazarin Gine-gine da Binciken Hanyoyi ta Najeriya

Durosimi Meseko, Shugaban Hukuma (Jihar Kogi)

22. Asibitin Koyarwa na Tarayya, Gombe

Zainab Ibrahim, Shugabar Hukuma (Jihar Taraba)

23. Hukumar kula da jiragen kasa ta kasa (NRC)

Dr. Kayode Opeifa, Manajan Darakta (Jihar Lagos)

24. Asibitin tarayya, Ido-Ekiti

Durotolu Bankole, Shugaban Hukuma (Jihar Ogun)

25. Cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Abeokuta

Mr. Dayo Israel, Shugaban Hukuma (Jihar Lagos)

26. Cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Asaba

Mary Idele, Shugabar Hukuma (Jihar Edo)

27. Cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Lokoja

Chidi Duru, Shugaban Hukuma (Jihar Anambra)

28. Cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Owerri

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

Emma Eneukwu, Shugaban Hukuma (Jihar Enugu)

29. Hukumar Tsaro, Shige da Fice, da Hukumar Kula da Gidajen Yari

Manjo-Janar Jubril Abdulmalik (mai ritaya), Sakataren Hukuma (Jihar Kano)

30. Cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Umuahia

Mr. Uguru Ofoke, Shugaban Hukuma (Jihar Ebonyi)

31. Cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Yenagoa

Felix Morka, Shugaban Hukuma (Jihar Delta)

32. Cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Yola

Bashir Gumel, Shugaban Hukuma (Jihar Jigawa)

33. Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya David Umahi, Uburu, Jihar Ebonyi

Dr. Ijeoma Arodiogbu, Shugaban Hukuma (Jihar Imo)

34. Shugaban Hukumar Binciken Kwararar Man Fetur ta kasa

Edward Omo-Erewa, Shugaban Hukuma (Jihar Edo)

35. Shugaban Hukumar Kula da Tsaron Ruwa ta Najeriya (NIMASA)

Yusuf Abubakar, Shugaban Hukuma (Jihar Kaduna)

36. Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Nnewi, Jihar Anambra

Ali Dalori, Shugaban Hukuma (Jihar Borno)

37. Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Shika, Zariya, Jihar Kaduna

Kara karanta wannan

Fitattun ƴan siyasar Kano 3 da Tinubu ya nada jagororin manyan hukumomin gwamnati

Lawal Liman, Shugaban Hukuma (Jihar Kaduna)

38. Cibiyar kiwon lafiya, Katsina

Dr. Abubakar Maiha, Shugaban Hukuma (Jihar Katsina)

39.Hukumar Binciken Sinadarin Sarrafa Kayayyaki ta Najeriya

Isa Achida, Shugaban Hukuma (Jihar Sokoto)

40. Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Birnin Kudu

Dr. Mohammed Hassan, Shugaban Hukuma (Jihar Zamfara)

41. Cibiyar Bincike Kan Gine-gine da Hanyoyi ta Kasa

Yahuza Inuwa, Shugaban Hukuma (Jihar Nasarawa)

42. Hukumar Raya Yankin Tafkin Kogin Sokoto-Rima

Abubakar Wurno, Shugaban Hukuma (Jihar Sokoto)

43. Asibitin Malam Aminu Kano

Augustine Umahi, Shugaban Hukuma (Jihar Ebonyi)

44. Hukumar Ba da Tallafin Karatu ta Tarayya

Babatunde Fakoyede, Shugaban Hukuma (Jihar Ekiti)

45. Asusun Ba Da Taimako da Inshora ta Najeriya.

Shola Olofin, Shugaban Hukuma (Jihar Ekiti)

Tinubu ya nada sababbin mukamai

A baya, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Cornelius Oluwasegun Adebayo, ɗan tsohon gwamnan Jihar Kwara a matsayin shugaban NALDA.

Cornelius Oluwasegun Adebayo shi ne ɗan marigayi Cif Cornelius Olatunji Adebayo, wanda ya yi gwamnan Jihar Kwara a shekarar 1983, kuma sanannen dan siyasa ne da ake damawa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel