Gwamnonin Arewa Sun Shiga Jimami da Tsohon Ministan Abuja Ya Rigamu Gidan Gaskiya
- Gwamnonin Arewa sun nuna alhinin rasuwar tsohon ministan Abuja, Lt. Gene. Jeremiah Useni, wanda ya rasu yana da shekaru 82
- Gwamna Inuwa Yahaya, shugaban NSGF, ya bayyana Useni a matsayin gwarzon kasa, mai kishin hadin kai da ci gaban Najeriya
- Gwamna Yahaya ya mika ta'aziyya ga Gwamna Caleb Muftwang, iyalai da al’ummar Filato, yana kira da a yi koyi da rayuwar marigayin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Gwamnonin Arewa karkashin kungiyar NSGF sun nuna jimami game da rasuwar tsohon ministan Abuja, Laftanar Janar Jeremiah Timbut Useni.
Shugaban kungiyar gwamnonin NSGF, kuma gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Source: Facebook
Matashiya: Lt. Gen. Useni ya rasu
Legit Hausa ta rahoto cewa Laftanar Janar Jeremiah Timbut Useni ya rasu a ranar Alhamis, 23 ga watan Janairun 2025 yana da shekaru 82 a duniya.
'Yan uwan marigayi Useni sun bayyana cewa tsohon ministan ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Daraktan yada labaran gwamnan jihar Filato, Gyang Bere ya fara sanar da labarin rasuwar Laftanal Janar Useni a shafinsa na Facebook.
Gyang Bere ya ruwaito gwamnan Filato, Caleb Mutfwang yana cewa mutuwar tsohon dan takarar gwamnan babban rashi ne ga iyalansa, rundunar soji, jihar Filato da kasa baki daya.
Gwamna Mutfwang ya bayyana marigayi Useni a matsayin jajurtaccen mutum wanda ya ginu a kan tabbatar da zaman lafiya da tsaro, musamman a jihar Filato.
Gwamnonin Arewa sun yi jimamin mutuwar Useni
Gwamna Inuwa, a madadin gwamnonin jihohin Arewa 19, ya bayyana marigayi Janar JT Useni a matsayin gwarzo kuma mai kishin kasa, inji rahoton Leadership.
Ya jaddada rawar gani da marigayin ya taka wajen ci gaban babban birnin tarayya, tare da kokarinsa wajen kawo hadin kai da ci gaban kasa.
A matsayin sanata mai wakiltar Kudancin Filato, marigayin ya bayar da gudunmuwa mai muhimmanci da za ta shiga cikin tarihi, inji Gwamna Inuwa.
“Laftanar Janar Useni ya kasance jagora mai martaba wanda ayyukansa a bangaren soja da farar hula suka yi tasiri sosai kan ci gaban Najeriya.”
- Gwamna Inuwa Yahaya.
Gwamnoni sun yiwa Filato ta'aziyya
Gwamna Inuwa ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Muftwang, gwamnatin Filato, al’ummar jihar, iyalan marigayin da abokan arziki.
Ya kuma bukaci iyalan marigayin da su yi koyi da rayuwar Useni wadda ta kasance cike da kishin kasa da son hidimtawa al’umma.
“Muna rokon Allah ya ji kansa, ya ba iyalai da masoyansa hakurin jure wannan babban rashi,” inji Gwamna Yahaya.
Janar Useni ya yi takarar gwamnan Filato
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta tsayar da Laftanar Janar Jeremiah Timbut Useni a matsayin dan takararta na gwamnan Filato a zaben 2019.
Janar Jeremiah Useni wanda a lokacin shi ne Sanatan Kudancin Filato ya lashe tikitin takara karkashin PDP bayan samun kuri'u 1, 018 a zaben fitar da gwani.
Asali: Legit.ng

