Janar Jeremiah Useni zai rikewa Jam’iyyar PDP tuta a zaben Gwamna

Janar Jeremiah Useni zai rikewa Jam’iyyar PDP tuta a zaben Gwamna

Labari ya zo mana cewa Laftanan Janar Jeremiah Timbut Useni (mai ritaya) ne zai yi takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP a Jihar Filato bayan ya samu tikitin Jam’iyyar a zaben da aka yi jiya.

Janar Jeremiah Useni zai rikewa Jam’iyyar PDP tuta a zaben Gwamna
Laftanan Janar Jeremiah Timbut Useni zai yi takarar Gwamna a 2019
Asali: UGC

Janar Jeremiah Useni wanda yanzu haka Sanatan Kudancin Filato ne zai rikewa Jam’iyyar PDP tuta a zaben Gwamnan Filato a 2019. Useni ya samu kuri’u 1, 018 ne a zaben inda Johnbull Shekarau ya zo na biyu da kuri’u 340.

Shi dai Sanata Janar Useini mai ritaya ya taba rike Ministan babban Birnin Tarayya da kuma Ministan sufuri a lokacin Gwamnatin Soja na Janar Sani Abacha. Sanatan dai zai gwabza da Gwamna mai-ci Simon Lalong na APC.

KU KARANTA: Wani Gwamnan Arewa na kokarin ficewa daga Jam’iyyar APC

Dattijon Sanatan mai shekaru 75 ya taba yin Gwamna a tsohuwar Jihar Bendel wanda ta kunshi Jihar Edo da Delta a lokacin Janar Muhammadu Buhari yana mulkin Soja. Sanatan na Filato ta Kudu dai zai jarraba sa’ar sa a zaben 2019.

Dazu kun ji cewa Sanata Suleiman Othman Hunkuyi da tsohon Shugaban NEMA sun fadi zaben fitar da gwani na takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar PDP a hannun Isah Ashiru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel