An Shiga Tashin Hankali da Wata Matashiya Ta Mutu a Hanyar Zuwa Sansanin NYSC
- Hatsarin mota ya kashe wata matashiya mai shirin yiwa kasa hidima yayin da take hanyarta ta zuwa sansanin NYSC a Ebonyi
- An rahoto cewa hatsarin ya rutsa da matasa masu shirin yiwa kasa hidima 12, amma matashiyar ce kadai ta mutu a nan take
- FRSC da NYSC sun tabbatar da faruwar hatsarin tare da bayyana jimamin abin da ya faru da matasan da ke shirin yiwa kasa hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ebonyi - Hatsarin mota ya yi ajalin wata matashiya mai shirin yiwa kasa hidima da ke a kan hanyarta ta zuwa sansanin NYSC na garin Afikpo, jihar Ebonyi.
Marigayiyar na cikin wasu matasa masu shirin yiwa kasa hidima 12 da ke a cikin wata motar haya mai daukar mutane 14 da hatsarin ya rutsa da ita.

Kara karanta wannan
Jirgin Max Air da ya tashi daga Legas zuwa Kano ya yi hatsari, an samu karin bayani

Asali: Twitter
Matashiya ta mutu a hanyar zuwa NYSC
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa matashiyar ta rasu sakamakon munanan raunuka da ta samu, yayin da sauran abokan tafiyarta da fasinjoji suka ji raunuka daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ce matasan sun hau motar ne a Enugu, inda suke kan hanyarsu ta zuwa sansanin NYSC da ke garin Afikpo don samun horon makonni uku.
Hatsarin ya faru ne lokacin da burkin motar da matasan ke ciki ya shanye kuma ta bugi wata motar daukar kaya da aka ajiye a gefen hanya.
An kwantar da sauran matasan a asibiti
Ana ganin matasan na cikin rukunin C Stream II na shekarar 2024 da ke shirin fara aikin yiwa kasa hidima.
Al'ummar yankin da jami'an tsaro sun ceci wadanda suka ji rauni daga cikin motar da ta yi kaca kaca sannan aka garzaya da su asibiti.
An ce kai wadanda hatsarin ya rutsa da su asibitin koyarwa na David Umahi (DUFUHS) don kula da lafiyarsu, inji rahoton jaridar Vanguard.
Shugaban FRSC ta tabbatar da hatsarin
Kwamandan hukumar FRSC na jihar Ebonyi, Igwe Henry, ya tabbatar da faruwar hatsarin, amma bai bayyana yawan wadanda suka mutu ba.
Igwe Henry ya ce:
“Lokacin da jami’anmu suka isa wurin, an riga an kai wadanda suka ji rauni asibiti.
"Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na rana, a kan hanyar Amasiri-Okiigwe, a kauyen Amenu, Okposi."
Shugabar NYSC a Ebonyi ta yi tsokaci
Motoci biyu ne hatsarin ya shafa: wata Toyota kirar bas mai launin toka da wata motar tifa ta daukar kaya kirar Mercedes-Benz.
Shugabar hukumar NYSC na jihar Ebonyi, Foluke Oladeinde, ta ce tana cikin yanayi na kaduwa saboda jin abin da ya faru da matasan.
"Ba zan iya magana yanzu ba, ina asibiti. Lallai hatsarin ya faru, amma ban shirya yin karin bayani ba a yanzu."
- A cewar Foluke.
An hukunta malama mai dukan 'yar NYSC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kwara ta rage matsayin malama Fatimoh Nike sakamakon fada a wurin aiki da kuma dukan wata matashiya mai yiwa kasa hidima.
Gwamnatin ta ce za ta tura malamar zuwa wata makaranta tare da ba ta horo kan kyawawan dabi’u domin inganta halayenta.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi alkawarin kare martabar NYSC tare da tabbatar da cewa irin wannan abu ba zai sake faruwa ba.
Asali: Legit.ng