'Karya ce': Malamin Musulunci Ya Musanta Kisan Ɗan Bello Turji, Ya Fadi Lokacin Aurensa
- Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan labarin kisan ɗan Bello Turji da ake yaɗawa
- Malamin ya musanta rahoton da ke cewa an kashe dan Bello Turji inda ya ce ba gaskiya ba ne, ya ce yana raye kuma yana cikin yankin Bawa a bakin iyakar Niger
- Ya ce tun kafin farmakin da aka kai, Turji ya samu labari ya tsere da kayansa daga inda ake zaton yana nan
- Wannan na zuwa ne bayan rahoton cewa rundunar sojoji ta yi nasarar hallaka matayan Turji da kuma ɗansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Sokoto - Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Murtala Bello Asada ya bayyana abin da ya sani game da labarin kisan ɗan Bello Turji da aka yi.
Malamin ya ce yaron rikakken dan ta'addan bai mutu ba inda ya yi kokwanton shekarunsa da hotonsa da ake yaɗawa.

Asali: Facebook
Sojoji sun sanar da kisan ɗan Bello Turji
Sheikh Asada ya fadi haka a cikin wani rubutu da kuma bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 23 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Sojojin Najeriya sun yi bayani bayan kashe ɗan ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji tare da wasu mayakansa yayin farmaki.
Dakarun soji sun lalata matattarar ‘yan ta’adda a yankin Fakai, Shinkafi da Kagara, tare da ceto mutane da aka yi garkuwa da su.
Manjo Janar Edward Buba ya bayyana Bello Turji a matsayin matsoraci bayan ya gudu ya bar ɗansa da mayakansa tare da sojoji.
Sheikh Asada ya musanta kisan ɗan Turji
A cikin rubutun, Shehin malamin ya musanta labarin kisan ɗan Bello Turji inda ya ce dan ta'addan ba shi da ɗa kamar haka.
Ya ce uwargidan dan ta'addan ba ta da babban yaro kamar wanda ake yaɗawa inda ya ce farfaganda ce.
"Maganar kisan ɗan Bello Turji farfaganda ce ta yan siyasa duk da akwai mutanen kirki da suka fada sai dai mu ce sun yi kuskure irin na dan Adam."
"Dalili shi ne uwar gidan Bello Turji ba ta da ɗa da ya kai shekaru 10 saboda bai wuce shekaru 15 da yin aure ba, shi ma kansa shekunsa ba su fi 35 ba."
- Sheikh Bello Asada
Maganar hari kan Bello Turji, malamin ya ce kafin kai harin ma dan ta'addan ya kashe komai na shi ya bar yankin.
Malamin ya koka kan yadda aka siyasantar da tashin tsaro da ta'addanci a Najeriya.
Shehi ya yi kwadayin mulkin Buhari
Kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada, ya magantu kan shirye-shiryen zaben 2027, yana jan hankalin al'umma kan abin da ke tafe.
Malamin ya koka kan yadda ake kokarin tallata Bola Tinubu a zaben 2027, yana fadin cewa Allah ya tarwatsa masu wannan shiri.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, malamin ya ce Allah ya taimaki masu nufin alheri, ya kuma magance masu son tada fitina.
Asali: Legit.ng