"Ba Zan Yi Sulhu ba Amma Ina da Mafita 1 ga Ƴan Bindiga," Gwamna Dikko Ya Yi Bayani
- Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zauna tattaunar sulhu da miyagun ƴan bindiga ba
- Sai dai gwamnan ya ce ƙofarsa a buɗe take ga ƴan ta'addan da suka yi tuba ta gaskiya, za ta taimaka masu su sake gina rayuwa a cikin al'umma
- Malam Dikko ya kuma yabawa ƴan sanda, sojojin sama da na ƙasa, dakarun hukumar NSCDC da jami'an tsaron da ya kirkiro bisa ƙoƙarin da suke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yaki da matsalar tsaro amma ba za ta taɓa sulhu da ƴan bindiga ba.
Malam Dikko ya faɗi hakan ne da kwamandan runduna ta 8 kuma kwamandan rundunar haɗin guiwa ta Arewa maso Yamma, Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose, ya kai masa ziyarar ban girma.

Asali: Facebook
Sakataren watsa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Muhammed ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manjo Janar Jose ya ziyarci mai girma gwamnan ne a gidan gwamnatinsa da ke Katsina ranar Laraba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Gwamna Radda ya nanata cewa ƙofar gwamnatinsa a buɗe take wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Gwamna Dikko ya kawo mafita ga ƴan bindiga
Ya ce gwamatinsa na iya tattaunawa da ‘yan bindiga amma a ƙarƙashin tsauraran sharuɗɗa tare da cikakken haɗin gwiwar al’umma.
“Gwamnatina ba za ta yi sulhu da masu aikata mugayen laifukan ta'addanci a jihar Katsina ba.
“Amma waɗanda suka tuba da gaske kuma suke neman komawa cikin al’umma, a shirye muke mu tallafa musu da duk abin da ya kamata don su sake gina rayuwa mai inganci.”
- Malam Dikko Raɗɗa.
Mstakan da gwamnan Katsina ya ɗauka
Don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, Dikko ya kafa kwamitin tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki domin jawo al’umma cikin shirin samar da zaman lafiya.
Gwamnatin Katsina ta kuma ɗauki alwashin haɗa ƴan bindigar da suka tuba cikin harkokin kiwon dabbobi da sauran sana’o’i masu amfani.
Gwamna Radda ya yi bayanin cewa jihar ta zuba jari mai yawa a bangaren kayan aikin tsaro, yana mai cewa Katsina na kan gaba a wannan fanni idan aka kwatanta da sauran jihohi.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da bayar da tallafin kayan aiki, ciki har da magance matsalar samar da man fetur, domin inganta ayyukan dakarun tsaro.
Dikko Radda ya jinjinawa jami'an tsaro
Malam Dikko ya yaba wa ƙoƙarin sojojin ƙasa, rundunar sojin sama, ‘yan sanda, hukumar NSCDC, da kuma askarawan Katsina, waɗanda suka yi aiki tare wajen inganta tsaro.
Ya kuma gode wa kwamandojin soji na rundunar Birged bisa jarumtar da suka nuna, yana mai cewa yanayin tsaro ya inganta kum manoma sun samu damar komawa gonakinsu da kai kaya kasuwa.
Wani jami'an rundunar CWC ta Katsina ya shaidawa Legit Hausa cewa babu zsncen sulhu a aikin da aka ba su umarnin yi na kare ƴan uwansu.
Jami'an wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ba za su yi ƙasa a guiwa sai sun ga bayan ƴan fashin daji da dukkan masu taimaka masu da ke rayuwa a cikin al'umma.
"Kamar yadda mai girma gwamna ya faɗa ba zancen sulhu, su fito a gwabza kawai mu a shirye muke mu mutu wajen kare ƴan uwa da iyalanmu," in ji shi.
Gwamnatin Katsina ta nesanta kanta da taron Batsari
A wani labarin, kun ji cewa gwammatin Katsina ta nesanta kanta daga dhiga wsta tattaunar sulhu da ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Batsari.
Gwamnatin ta bayyana cewa babu sa hannunta a wannan zama kuma ba za ta fana yin sulhu da ƴan ta'adda ba.
Asali: Legit.ng