Sojoji na Daf da Cimma Bello Turji, an Kashe Mataimakinsa, Aminu Kanawa

Sojoji na Daf da Cimma Bello Turji, an Kashe Mataimakinsa, Aminu Kanawa

  • Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe Aminu Kanawa, na hannun daman dan ta'adda, Bello Turji, yayin farmakin da aka kai tsakanin 20 zuwa 21 ga Janairu
  • An kuma kashe wasu manyan mayakan Turji, ciki har da Jabbi Dogo, Dan Kane, Kabiru Gebe, da Suleiman, wanda ya yi yunkurin kare sansanin Turji a Fakai
  • Sojoji sun ce nasarar ta kawo gagarumin koma baya ga 'yan ta'adda a jihohin Zamfara da Sokoto, inda sojojin suka ce za su ci gaba da kai hare-hare

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Rundunar Sojojin Najeriya ta samu nasarar kashe Aminu Kanawa, wanda aka bayyana a matsayin na hannun daman fitaccen shugaban 'yan ta'adda, Bello Turji.

An kashe Aminu Kanawa ne a wata gagarumar fafatawa da aka yi tsakanin 20 zuwa 21 ga watan Janairu 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Turji
An kashe mataimakin Bello Turji. Hoto: HQ Nigerian Army|Hassan Abdullahi
Asali: Facebook

Rahoton Channels Television ya nuna cewa daraktan yada labaran rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kara da cewa an kashe wasu daga cikin manyan mayakan Turji da suka hada da Abu Dan Shehu, Jabbi Dogo, da Kabiru Gebe, yayin farmakin da aka kai sansaninsu.

Yadda aka kashe mataimakin Turji

A cewar Manjo Janar Edward Buba, sojoji sun kashe Aminu Kanawa ne a yayin wani gagarumin farmaki da aka kai sansanin Turji a kusa da Gebe da karamar hukumar Isa ta Jihar Sokoto.

An kuma kashe wasu mayakan da suka hada da Basiru Yellow, Bello Buba, da Dan Inna Kahon-Saniya-Yafi-Bahaushe.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa suna daga cikin masu shirya hare-haren ta'addanci a jihohin Zamfara da Sokoto.

Manjo Janar Buba ya kara da cewa sojojin sun kashe fiye da 'yan ta'adda 24 da suka yi yunkurin tserewa daga sansanin Turji.

Kara karanta wannan

Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin

An kashe wanda zai kare maboyar Turji

Sanarwar ta kara da cewa wani sanannen dan ta'adda mai suna Suleiman, wanda ya jagoranci tawaga domin taimakawa sansanin Turji a yankin Fakai, ya rasa ransa yayin arangama da sojoji.

Suleiman ya kasance mabiyin Halilu Sububu, wani tsohon shugaban 'yan ta'adda da aka kashe a baya, ya rasa rayuwarsa a yayin da yake kokarin dakile farmakin sojoji.

Manjo Janar Buba ya ce;

“Mutuwar Suleiman da sauran mayakan Turji babbar nasara ce da ta rage karfin kungiyar ta'addanci a yankin.”

Nasarar sojoji wajen ruguza ta'addanci

Daraktan yada labaran ya bayyana cewa nasarar da aka samu a kan Turji babbar koma baya ce ga 'yan ta'adda, inda ya ce hakan zai rage yawan hare-haren da ake kai wa.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai hare-hare domin ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Kara karanta wannan

Sojoji 22 sun rasu bayan kashe Boko Haram 70 a wani kazamin fada

Neman goyon bayan al'ummar kasa

Sojojin Najeriya sun bukaci al’ummar yankin Arewa maso Yamma su ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ta hanyar ba da bayanan sirri game da maboyar ‘yan ta’adda.

Rundunar ta ce burinta shi ne tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga kowa da kowa, ba tare da barazana daga 'yan ta'adda ba.

An kashe 'yan bindiga 7 a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta kashe masu manyan 'yan ta'adda 7 yayin musayar wuta a jihar Katsina.

Haka zalika rundunar ta bayyana nasarar ceto yara sama da 200 da aka yi safarar su a jihohi ciki har da jariri dan kasa da kwanaki 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel