An Sako Abba a Gaba saboda 'Kashe' N2.3bn a Rabon Awaki, Gwamnatin Kano Ta Yi Bayani

An Sako Abba a Gaba saboda 'Kashe' N2.3bn a Rabon Awaki, Gwamnatin Kano Ta Yi Bayani

  • Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin raba awaki ga mata 2,000 a jihar, tana mai cewa tsare-tsaren ilimi ne ke jagorantar wannan shiri
  • Hukumar kididdiga ta jihar ta tabbatar da cewa rabon akuya zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin mata da bunkasa tattalin Kano
  • Jimillar naira biliyan 2.3 ne aka ware domin aikin gaba daya, wanda zai hada da raba shanu, tumakai da sauran abubuwan kula da kiwo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi karin bayani kan rabon awaki 7,150 da aka yi wa mata 2,000 a jihar, tana mai cewa wani bangare ne na shirin bunkasa kiwon dabbobi da tallafa wa mata.

Babban jami’in kididdiga na jihar Kano, Dr, Aliyu Isa Aliyu, ya ce rabon ya biyo bayan rahoton kididdigar kasa na 2024 da ya nuna cewa jihar Kano na da kaso mai tsoka a bangaren kiwo.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Awaki
Gwamnatin Kano ta yi karin bayani kan raba akuya. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Dr Aliyu ya bayyana cewa wannan tsari zai karfafa tattalin arziki tare da bunkasa rayuwar mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kididdiga kan muhimmancin kiwo

Dr Aliyu Isa Aliyu ya bayyana cewa yankin Arewa maso Yammacin Najeriya yana samar da kashi 33% na jimillar kiwon dabbobin kasar, inda jihar Kano ke da kaso 8% na wannan adadi.

“A cewar rahoton kididdigar kasa, Najeriya na da jimillar akuya miliyan 16.59, kuma jihar Kano na da kimanin akuya miliyan 1.458.
Hakan ya sanya Kano ta kasance ta biyu a fannin kiwon dabbobi bayan jihar Bauchi.”

- Dr Aliyu Isa Aliyu

Shugaban ya kara da cewa jihar Kano ita ce kan gaba wajen yawan gidajen gona a Najeriya, wanda hakan ya sa shirin rabon akuya ke da muhimmanci ga jihar.

Misalai daga tarihi da shawarwari

Dr. Aliyu ya kawo misalin shirin kiwon macizai da kwadi da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Saminu Turaki, ya gabatar a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

“A lokacin da Saminu Turaki ya gabatar da wannan shiri, an dauka kamar ba shi da hankali,
"Amma idan da mutane sun rungumi wannan tsari, da yanzu Jigawa na daya daga cikin manyan masu fitar da macizai da kwadi a duniya.”

- Dr Aliyu Isa Aliyu

Ya yi kira ga al’ummar Kano su kalli shirin kiwon akuya da tsari na dogon lokaci domin ganin irin tasirin da zai yi ga tattalin arzikin jihar.

Bayani sayen akuya a kan Naira biliyan 2.3

Aliyu ya karyata rade-radin cewa an kashe N2.3bn kan sayen akuya kawai, ya ce wannan kudin an ware shi ne domin aiwatar da gaba dayan tsare-tsaren bunkasa kiwo a jihar.

Ya ce shirin zai gudana a matakai uku:

1. Matakin farko: Rabon akuya 7,150 ga mata 2,000

2. Mataki na biyu: Rabon shanu 1,342

3. Mataki na uku: Rabon tumakai 1,822

Kara karanta wannan

'Annabi ya fadi amfanin namansu ga lafiya': Abba Kabir ya kare matakin raba awaki a Kano

Ya ce duk wanda ke da korafi ya kamata ya kalli shirin a gaba daya, ba wai ya tsaya kan rabon akuya ba kawai.

Dr. Aliyu ya jaddada cewa gwamnatin Kano tana bin tsare-tsaren da suka dogara da ilimi da bincike domin aiwatar da duk wasu manufofi.

Ya yi kira ga mutane da su daina kallon abin daga bangare guda, su yi tunani mai zurfi kan tasirin wannan shiri wajen bunkasa tattalin arzikin jihar.

Abba ya kwace filayen da Ganduje ya raba

A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya sanar da kwace filayen da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya raba.

Rahotanni sun nuna cewa Abba zai kwace filayen ne saboda an raba su ba bisa ka'ida ba domin kara aikin ginin tashoshin mota da Rabi'u Kwankwaso ya fara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel