Gwamnatin Jigawa Ta Raba Wa Mata Tallafin Akuya Da Bunsuru 4,050 Don Kawar Da Talauci

Gwamnatin Jigawa Ta Raba Wa Mata Tallafin Akuya Da Bunsuru 4,050 Don Kawar Da Talauci

  • Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba wa mata akuyoyi guda 4,050 a don karfafa musu gwiwa da kawar da talauci
  • Wannan shine karo na uku da gwamnatin na Jigawa ke yin rabon akuyoyin inda ta ce rabon na baya ya haifar da da mai do
  • Hasina Muhammad Abubakar, matar gwamnan Jigawa ta ce wasu jihohi da kungiyoyin kasa da kasa sun fara koyi da tsarin

Jihar Jigawa - A wani mataki na karfafa wa mata gwiwa da rage talauci, gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da rabawa mata akuyoyi 4,050 wanda shine karo na uku a tsarin, rahoton Leadership.

Da ya ke magana a wurin kaddamar da shirin raba akuyoyin ga wasu wadanda suka amfana a karamar hukumar Kazaure na jihar, matar gwamnan jihar, Hajiya Hasina Muhammad Abubakar ta ce rabon akuyoyin da aka yi a baya ya haifar da da mai ido.

Kara karanta wannan

Mahara Sun Banka Wa Gidaje 10 Wuta A Wani Unguwa A Kano

Taswirar Jihar Jigawa
Gwamnatin Jigawa Ta Rabawa Mata Akuyoyi 4,050 Matsayin Tallafi. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Ta yi bayanin cewa an kaddamar da shirin a karon farko ne a shekarar 2016 don taimakawa mata samun kudin shiga ta hanyar kiwon akuyoyi, tsarin ya bunkasa har ta kai ga wasu gwamnatoci da masu bada tallafi na kasa da kasa suna kwaikwayo.

Ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna alfahari da wannan tsarin na amfani da akuyoyi don karfafawa mata gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa ta fara wanda yanzu ya zama abin koyi ga wasu.
"Don haka, za mu cigaba da amfani da shi wurin karfafawa matan mu da kirkirar aikin yi, karfafa samar da nama da kawar da talauci."

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Leadership ta ruwaito cewa jama'a sun yi gangami a wuraren bada kudi a karamar hukumar Kiyawa ta jihar.

Kara karanta wannan

Dan a mutun Peter Obi ya samu lambar yabo a kasar Tanzania bayan kafa tura a Kilimanjaro

A cewar rijistan rabon kudin, sama da talakawa mutum 167,620 ake sa ran za su samu rabonsu cikin N1.6 billion.

Rahoton ya kara da cewa mutane sun tafi wajen da katunansu domin karban kudi.

Mata za su samu tallafin akuyoyi da bunsuru 47,544 daga gwamnatin jihar Jigawa

Gwamna Muhammadu Badaru na jihar Jigawa ya ce gwamnatinsa za ta rabawa mata 15,848 akuyoyi 47,544 a watan Yunin 2019 a karkashin shirin kiwon akuyoyi na Bankin bayar da bashi ga masu karamin karfi na jihar.

Badaru wanda ya yi magana da manema labarai a ranar Litinin a Dutse ya ce wannan tallafin yana cikin shirin jihar na tallafawa al'umma ta fanin kiwon dabobi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel