Jerin Muhimman Abubuwa da Najeriya Za Ta Mora bayan Shiga Kungiyar BRICS

Jerin Muhimman Abubuwa da Najeriya Za Ta Mora bayan Shiga Kungiyar BRICS

  • Najeriya ta samu shiga a matsayin mamba a ƙungiyar BRICS, domin inganta tattalin arziki na duniya daga kasashen da ke tasowa
  • Ƙungiyar BRICS ta ƙunshi Brazil, Rasha, India, China, da Afirka ta Kudu, Iran, Misira, Habasha da UAE a shekarar da ta gabata
  • Shigar Najeriya cikin BRICS zai buɗe hanyoyin zuba jari, haɓaka ci gaban tattalin arziki, da ƙarfafa rawar Najeriya a fagen duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Najeriya ta shiga ƙungiyar BRICS a matsayin mamba a ƙungiyar BRICS domin inganta tattalin arzikinsu da ke haɗa kasashen da ke tasowa.

Brazil, wanda ke shugabantar BRICS a yanzu, ta bayyana cewa muradun Najeriya suna daidai da na sauran mambobin ƙungiyar.

Moriyar da Najeriya za ta samu bayan shiga kungiyar BRICS
Fa'idojin da Najeriya za ta samu da ta shiga kungiyar BRICS. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Shekarar da aka kafa kungiyar BRICS

An kafa BRICS a 2009 da kasashe kamar Brazil, Rasha, India, da China don su zama tamkar kishiya ga ƙungiyar G7 ta manyan ƙasashe masu cigaba, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Afirka ta Kudu ta shiga ƙungiyar BRICS mai ma'anar Brazil, Rasha, Indiya, China, da Afirka ta Kudu a 2010, ƙungiya ce mai tasiri ta tattalin arzikin duniya.

A bara, an faɗaɗa ƙungiyar da shigar Iran, Misira, Habasha, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Da zuwa Najeriya, BRICS yanzu tana da ƙasashe tara kamar Belarus, Bolivia, Cuba, Kazakhstan, Malaysia, Thailand, Uganda, Uzbekistan, da Najeriya.

Wannan matakin zai ƙarfafa haɗin kai tare da ƙirƙirar damarmaki na ci gaban tattalin arziki da haɗin kai na dabarun Najeriya.

Legit Hausa ta duba fa'idodin da Najeriya za ta samu a kungiyar BRICS

1. Cigaban tattalin arziki

Jami’an Najeriya na fatan samun karin cinikayya da ƙasashen BRICS, musamman a bangaren man fetur, iskar gas, aikin gona, da masana’antu.

Hakan zai taimaka wa kasar wurin inganta tattalin arzikinta da ke kara dagulewa tun bayan hawan Bola Tinubu.

2. Zuba jari kai tsaye

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

Wannan haɗin gwiwa zai kawo habaka zuba hannun jarin kasashen waje daga ƙasashen BRICS, don tallafa wa muhimman ayyukan more rayuwa da samar da ayyukan yi.

Yayin da Najeriya ke ci gaba da neman hanyar inganta tattalin arzikin kasar, wannan mataki zai tallafa wa Najeriya, cewar Nairametrics.

3. Cigaban fasaha

Samun damar amfani da fasahohin zamani daga ƙasashen BRICS zai iya hanzarta ci gaban Najeriya a sassan makamashi mai sabuntawa, kayan aikin zamani, da binciken sararin samaniya.

Wannan matakin zai ƙara damar ci gaba a tattalin arziki, zuba jari, da haɗin kai na dabaru tare da ƙarfafa rawar Najeriya a fagen duniya.

4. Karin tasiri a idon duniya

Tare da shiga BRICS, Najeriya za ta sami damar yin tasiri a tattaunawar duniya, da kuma ƙarfafa matsayinta wajen yanke shawara na duniya.

Masana na ganin hakan zai kara wa Najeriya mutunci a idon duniya da kuma kara samun tasiri.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Ƙalubalen da ke gaban Najeriya

Duk da fa’idodin da aka ambata, Najeriya za ta fuskanci ƙalubale wajen daidaita dangantaka da kawayenta na kasashen Yamma tare da zurfafa haɗin kai da BRICS.

Domin gujewa dogaro ga wata ƙungiya guda ɗaya, Najeriya na buƙatar faɗaɗa haɗin kai tare da kasashen duniya don rage hatsarori masu yiwuwa.

Najeriya ta fadi dalilin kara kudin kiran waya

Kun ji cewa Ministan sadarwa da tattalin yanar gizo, Bosun Tijani ya kare karin kudin sadarwa yayin da gwamnati ke fuskantar barazanar shari’a.

Bosun Tijani ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan aiki da tsadar shigo da kayayyaki daga ketare ne suka jawo karin kudin waya, sako da data.

Kungiyar SERAP da NATCOMS sun yi barazanar kai gwamnatin tarayya kotu domin neman a janye karin kudin da suka ce ba bisa ka’ida yake ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.