'Yan Kwadago Sun Fara Bugawa da Tinubu kan Karin Kudin Fetur

'Yan Kwadago Sun Fara Bugawa da Tinubu kan Karin Kudin Fetur

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta yi magana bayan samun karin farashin fetur a Najeriya, ta ce akwai rashin tausayi ga talakawa a lamarin
  • Hakan na zuwa ne yayin da aka samu karin farashin mai a matatar Dangote sakamakon karin tsadar danyen mai a kasuwar duniya
  • NLC ta yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu da ta rika shawara da masu ruwa da tsaki kafin yanke muhimman matakai da suka shafi kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar 'yan kwadagon Najeriya (NLC) ta yi Allah-wadai da karin kudin litar man fetur zuwa tsakanin N1,050 da N1,150.

Kungiya NLC ta ce wannan matakin ya nuna rashin tausayi ga talakawa da ke fama da wahalhalun rayuwa.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

Yan kwadago
'Yan kwadago sun nuna fushi ga Tinubu kan karin kudin mai. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Wani shugaban kwadago ya bayyana hanyoyin da ya kamata gwamnati ta bi yayin da aka samu yanayi da ake da alaka da kara kudin fetur a hirar da ya yi da jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin farashin fetur da matsayin NLC

Shugabannin NLC sun bayyana cewa karin farashin man fetur ba wai kawai zai shafi farashin abinci da sufuri ba ne, har ma zai kara tsananta hauhawar farashin kaya da rage darajar Naira.

Mataimakin shugaban sashen siyasa na NLC, Farfesa Theophilus Ndubuaku ya ce gwamnati ba ta tuntubar masu ruwa da tsaki ba kafin daukar irin matakan.

“A matsayinka na shugaba, ya kamata ka gayyaci wakilan ma’aikata, kungiyoyi masu zaman kansu, da dalibai domin tattauna tasirin wannan mataki,”

- Farfesa Ndubuaku

Ya kuma bayyana cewa karin farashin ba wai zai kawo saukin rayuwa ba ne, sai dai karin wahala ga talakawa.

Tsadar danyen mai da matsayar kamfanoni

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun sanar da saukar farashin fetur bayan karyewar abinci

Matatar Dangote ta bayyana cewa karin farashin man fetur ya samo asali ne daga tsadar danyen mai a kasuwannin duniya.

Masu sana’ar man fetur sun ce tsadar danyen mai ce ta haifar da karin kudin sarrafa mai, wanda hakan ke sanya farashin man fetur ya ci gaba da hawa.

Amma NLC ta zargi masu sayar da man fetur da amfani da wannan damar wajen kara farashi domin cin kazamar riba.

Shugabar NLC a Legas, Sessi Funmi ta bayyana masu sayar da man a matsayin “makiyan talakawa” tare da zargin su da kokarin kawo cikas ga gwamnati wajen sauke farashi.

Kiran NLC kan tattaunawa da jama’a

Farfesa Ndubuaku ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta dauki matakan tattaunawa da jama’a kafin yanke shawarar da za ta shafi rayuwar talakawa.

Ya kuma yi nuni da yadda tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ke shirya tarukan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnati a duk wata.

Kara karanta wannan

Malamin da ya je Nijar ya ce sojoji sun tsananta tsaro, ya gargadi 'yan Najeriya

“Ba ma cewa ka da ku dauki matakan da suka dace. Amma dole ne ku sanar da jama’a dalilan da ke bayan irin wannan mataki domin su fahimci inda aka dosa,”

- Farfesa Ndubuaku

Har ila yau, shugabar NLC ta Jihar Legas ta yaba wa gwamnatin Tinubu kan kokarinta na farfado da matatun mai biyu da ke Fatakwal da Warri.

Tinubu zai raba kudi ga 'yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara wani shiri na musamman domin rage radadin talauci ga 'yan Najeriya.

A karkashin shirin, za a rika raba kudi har N75,000 ga miliyoyin 'yan Najeriya domin yaki da fatara da talauci a fadin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel