Musulmai da Kirista Sun Ajiye Faɗan Addini, Sun Dawo Zama a Gari 1 bayan Shekara 23

Musulmai da Kirista Sun Ajiye Faɗan Addini, Sun Dawo Zama a Gari 1 bayan Shekara 23

  • Al’ummar Musulmi da Kirista na garin Gangare sun sasanta kansu, sun dawo zama wuri daya bayan shekaru 20 da rikicin Jos
  • Shugabannin addinan biyu sun yaba da sasancin da aka yi, suna mai cewa zaman lafiya ya zama wajibi don ci gaban al’umma
  • Shugaban garin Gangare ya bayyana matsayar da addinan suka cimmawa a matsayin matakin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Mazauna garin Gangare da ke Jos ta Arewa, jihar Filto sun sake dawowa garuruwansu bayan rikicin addini na 2001 da ya faru a Jos.

Rikicin addini na 2001 ya bazu zuwa wasu garuruwan da ke ciki da wajen Jos, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Malaman addini sun yi magana yayin da aka samu zaman lafiya a Jos bayan rikicin 2001
An samu daidaito tsakanin Musulmi da Kirista a Jos bayan shekaru karni 2 da rikicin addini. Hoto: Gangare Youths Forum
Source: Facebook

Bayan rikicin, al’ummar Jos, musamman Musulmi da Kirista na garin Gangare, sun shata iyakar wurin zama tare da kauracewa juna, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jos: Musulmi, kirista sun shaida zaman lafiya

A kokarin dawo da zaman lafiya, Kiristoci da Musulman Gangare sun shirya taron hadin kai mai suna "taron sake hadin kan mazauna Gagare"

Gangare John, Fasto na Cocin ECWA, ya ce:

“Mun zauna lafiya kafin rikicin. Amma an tilasta ni tashi da iyalaina daga Gangare sakamakon rikicin, amma yanzu wannan taron ya faranta mani rai.”

Limamin masallacin Gagare, Aliyu Aliyu ya ce:

“Yau rana ce ta tarihi, domin mun fara dawo da hadin kai a tsakaninmu. Sanin kowa ne addini bai koyar da mu rikici ba.
“Rikicin 2001 ya faru ne sakamakon son zuciya da wasu suka dauka, amma ba koyarwar addini ba ne.”

Mazauna Gangare sun ji dadin wannan sasanci

Martha Dauda, tsohuwar mazauniyar Gangare, ta ce ta haifi 'ya'yanta takwas a garin kafin ta koma wani garin saboda wancan rikicin.

Martha ta ce:

“Ba za mu samu zaman lafiya ba sai iyaye sun koyar da yara muhimmancin zaman lafiya. Addini bai koyar da tashin hankali ba.”

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

Wata mazauniyar Gangare, Justina Beguwan ta ce:

“Na taso a Gangare. Bayan rikicin muka koma wani garin na daban, amma yau mun dawo zaman 'yan uwa da muka saba.”
“Ko da can, muna zama a wuri ɗaya tamkar 'yan uwa. Bambancin addini ba zai raba mu ba, domin Allah ne ya halicce mu duka.”

Shugaban Gangare ya yi muhimmiyar magana

Usman Ali, shugaban garin Gangare, ya bayyana muhimmancin wannan rana da kuma taron hadin kan da aka gudanar.

Shugaban ya ce:

“An haife ni kuma na girma a garin Gangare. Kiristocin da suka halarci wannan taron ko dai ’yan tsararrakinmu ne ko kuma na kasa da mu ne. Amma dai duka a garin nan aka haife mu.
“Mun samu taimakon Allah wajen ganin mun dawo da kowa kusa da juna. Wannan zai kawo zaman lafiya a garinmu da jihar baki daya.”

Da yake magana kan taron, ya ce yana fatan wannan haɗin kai zai kawo ƙarshen rarrabuwar kawuna da bude sabon babin zaman lafiya mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

"Ba za mu yarda da rikicin addini ba" - Lalong

A wani labarin, mun ruwaito cewa Simon Lalong, a lokacin da ya ke gwamnan Filato, ya ce gwamnatinsa za su yi duk mai yiwuwa don dakile rikicin addini a jihar.

Simon Lalong ya ce ba zai lamunci rikicin addini ba yayin da ya yi alkawarin cewa duk wadanda ke da hannu a rikicin da ke faruwa zai fuskanci hukunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com