Ba za mu yarda a sake samun rikicin addini a Filato ba, in ji Lalong

Ba za mu yarda a sake samun rikicin addini a Filato ba, in ji Lalong

  • Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci dawowar rikicin addini a jihar ba
  • Lalong ya bayyana cewa suna kokari tare da hukumomin tsaro wajen yin duk mai yiwuwa don dakile rikicin addini a jihar
  • Ya kuma sha alwashin hukunta duk wadanda aka samu da hannu a rikicin baya-bayan nan

Jos, Filato - Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su yi duk mai yiwuwa don dakile rikicin addini a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Gwamnan ya yi magana ne a ranar Litinin lokacin da ya zagaya sassan Jos ta Arewa don sa ido kan bin dokar hana fita na sa’o’i 24.

Ba za mu yarda a sake samun rikicin addini a Filato ba, in ji Lalong
Gwamna Simon Lalong ya ce ba za su yarda jihar Filato ta koma rikici irin na baya ba Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Lalong ya sha alwashin cewa za a hukunta duk wadanda ke da hannu a rikicin na baya -bayan nan sosai.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Ya kuma bayyana cewa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Jos ta Arewa za ta ci gaba, yayin da dokar hana fita ta yamma zuwa wayewar gari a Jos ta Kudu da Bassa su ma za su ci gaba da kasancewa har sai baba-ta-gani, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan jihar ya ziyarci asibitoci inda ake kula da yawancin mutanen da suka jikkata a hare -haren baya -bayan nan a jihar. Ya kuma zagaya wurare a Jos, babban birnin jihar, wadanda fadan ya shafa.

An tattaro cewa daliban jami’ar Jos uku sun mutu, wasu biyu sun bace a harin da aka kai wa matafiya a hanyar Rukuba a ranar Asabar, wanda ya kai ga kashe matafiya sama da 20.

Gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita a Jos bayan hare -haren.

Kara karanta wannan

Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamnan Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jiharsa

Jihar ta fada cikin rikici a shekarun 2000 wanda har yanzu take fama da tabonsu.

Gwamna Lalong tare da rakiyar mataimakinsa, Prof. Sonny Tyoden, membobin majalisar zartarwa da shugabannin tsaro sun ziyarci asibitin koyarwa na jami’ar Bingham Jos inda ake kula da wadanda suka jikkata a hanyar Rukuba da sauran hare -hare.

Ya kuma ziyarci Cocin Redeemed Christian Church of God da ke kan titin Bauchi wanda wasu ‘yan daba suka kona wani bangare kafin al’umma su tashi don kare cibiyar bautar.

Gwamna Lalong ya kuma ziyarci Asibitin Kwararru na Filato inda aka gaya masa cewa yawancin marasa lafiyar suna samun sauki.

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

A baya mun kawo cewa Simon Lalong, gwamnan jihar Filato ya bayar da umarnin damke duk wanda yayi gaggawar zuwa belin wandanda aka kama ana zargin suna da hannu a kan farmakin jiharsa.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Gwamnan jihar ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron gaggawa da yayi da manyan jami’an tsaro a Jos, Thecable.ng ta ruwaito.

Kamar yadda NAN ta ruwaito, an yi taron na musamman ne a ranar 14 ga watan Augusta akan harin da aka kai karamar hukumar Bassa, Jos ta kudu, Barikin Ladi da Riyom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng