Yaki da Rashin Aikin yi: Gwamna Zai Dauki Ma'aikata 3,000

Yaki da Rashin Aikin yi: Gwamna Zai Dauki Ma'aikata 3,000

  • Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya amince da daukar malamai 3,000 domin kara ma'aikata a makarantun sakandare na jihar
  • An ruwaito cewa hirin yana cikin tsare-tsaren AGILE na bunkasa ilimi, musamman ga ‘ya'ya mata, tare da ba su da tallafin kudi
  • Rahotanni sun nuna cewa za a fara biyan kudin tallafin ilimi ga dalibai mata 9,000 a makarantu cikin makonni biyu masu zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin jagorancin gwamna Bala Mohammed ta dauki sabon mataki na bunkasa ilimi a jihar, inda ta amince da daukar malamai 3,000.

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a dauki malaman ne domin kara karfafa koyarwa a makarantun sakandare na jihar.

Bala Mohammed
Za a dauki malamai 3,000 a Bauchi. Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa gwamnatin Bauchi ta fitar da sanarwar ne a lokacin wani shirin AGILE na tallafawa 'ya'ya mata a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya ayyana dokar ta ɓaci a jiharsa, zai ɗauki malamai 2,000 aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a rarraba malamai a makarantu

Shugaban shirin AGILE a jihar, Ali Gar, ya bayyana cewa malamai 2,000 daga cikin adadin za su rika koyarwa a makarantun karamar sakandare.

Ali Gar ya kara da cewa sauran malamai 1,000 za su rika koyarwa a manyan makarantun sakandare na jihar Bauchi.

A cewar Ali Gar;

“Za a dauki malamai daga yankuna da ke kusa da makarantu domin tabbatar da saukaka zirga-zirga, kulawa, da kuma tabbatar da cewa suna aiki yadda ya kamata."

Ya kuma bayyana cewa dukkan malaman da za a dauka za su kasance karkashin biyan albashin gwamnatin jihar Bauchi ne, ba shirin AGILE ba.

Raba tallafin kudi ga dalibai mata

A wani bangare na shirin, za a fara biyan tallafi ga dalibai mata 9,000 a makarantun jihar cikin makonni biyu masu zuwa.

Shirin ya kunshi raba:

  • N15,000 a matsayin kudin rajista
  • N10,000 a matsayin kudin kashewa a zangon farko
  • N20,000 matsayin kudin kashewa a zango na biyu da na uku

Kara karanta wannan

2027: Rikici ya barke tsakanin gwamnan Bauchi da ministan Tinubu

Sai dai an kafa sharadin cewa dole dalibai su halarci a kalla kashi 75% na darussa kafin samun tallafin.

Ali Gar ya bayyana cewa, dukkan kayan aikin ICT da na koyon sana’o’i da ake bukata domin aiwatar da shirin sun iso kuma an raba su.

Daily Post ta wallafa cewa shugaban shirin ya ce sun samu nasarar zakulo dalibai mata 9,000 daga cikin 20,250 da aka yi niyyar tallafawa a cikin makonni goma.

Yadda za a kula da aikin malamai

Gwamnatin jihar ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki su sanya idanu kan ayyukan malamai a mazabunsu, domin tabbatar da cewa suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Haka zalika, shugaban karamar hukumar Bauchi, Mahmood Babama’aji, ya yaba wa tawagar fasaha ta AGILE bisa kokarin da take yi wajen tabbatar da nasarar shirin.

“Ina da yakinin cewa mambobin kwamitin kula da makarantun za su cika alkawuran da aka sanya musu.”

Kara karanta wannan

Abba ya kwato motocin da jami'an gwamnatin Ganduje suka tsere da su a Kano

- Mahmood Babama’aji

Gwamnan Bauchi zai cigaba da sukar Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Bala Mohammed ya bayyana cewa zai cigaba da sukar tsare tsaren Bola Tinubu da suke kawo a matsala a tunaninsa.

An ruwaito cewa Sanata Bala Mohammed ya bayyana haka ne yayin ganawa da Fasto Johnson Suleman a fadar gwamnatin jihar Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng