'Sun Nemi N25m': Ƴan Sanda Sun Kama Mutanen da Suka Kashe Yaro a Katsina
- 'Yan sanda sun kama Muttaka Garba da Yusuf Usman bisa laifin garkuwa da kisan wani yaro dan shekara 12 a jihar Katsina
- Mutanen biyu sun nemi Naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa, amma suka kashe yaron bayan iyayensa sun gaza biyan kudin
- Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu bayan da suka shiga hannu, inda rundunar ta bayyana matakin da za ta dauka na gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Rundunar 'yan sandan Katsina ta bayyana cewa ta yi nasarar kama wanda ake zargin suna da hannu a garkuwa da mutane.
Rundunar ta ce an kama mutane biyu kan zargin sace wani yaro dan shekara 12 a garin Dankama da ke jihar da kuma kashe shi.
Kakakin 'yan sandan Katsina, DSP Abubakar Sadiq, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda mutane 2 suka kashe yaro a Katsina
Yayin da ake holen wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar a ranar Laraba, DSP Abubakar ya ce an sace yaron Salihu Sadi, a ranar 11 ga watan Janairu, 2025.
DSP Abubakar ya ce mutanen biyu sun sace yaron da misalin karfe 8:00 na yamma yayin da yake hanyar sayowa mahaifiyarsa magani.
Ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun kira 'yan uwan yaron bayan sun sace shi.
A cewar DSP Abubakar, masu garkuwar sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 25, amma iyayen yaron suka nuna ba su da wadannan kudade.
Kakakin 'yan sandan ya ce duk da kokarin 'yan uwan yaron na tattaunawa da masu garkuwar, abin ya ci tura, a karshe suka kashe yaron tare da wulakanta sassan jikinsa.
'Yan sanda sun kama wadanda ake zargi
An rahoto cewa an tsinci gawar yaron a bayan garin Dankama.
Sanarwar DSP Abubakar ta ce:
"Bayan samun rahoto, kwamishinan 'yan sandan Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya umarci sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar (AKU) da ya gudanar da bincike mai zurfi.
"A yayin gudanar da binciken, jami'an 'yan sanda a ranar 13 ga Janairu, 2025, sun gano kuma sun kama wadanda ake zargin guda biyu.
"Wadanda aka kama su ne; Muttaka Garba, wanda aka fi sani da Auta, mai shekaru 24, da kuma Yusuf Usman, wanda aka fi sani da Kwalwa, mai shekaru 20."
Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu
Sanarwar ta ce dukkanin wadanda ake zargin sun amsa laifin da suka aikata, inda suka tabbatar da cewa su ne suka sace yaron da kashe shi.
Rundunar 'yan sanda ta samu wayar da aka yi amfani da ita wajen neman kudin fansar, wanda yanzu haka ana amfani da ita a matsayin hujja a binciken da ake yi.
Sanarwar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan kammala binciken da ake yi.
Wannan kamen na daya daga cikin nasarorin da rundunar 'yan sanda ta samu a cikin makon da ya gabata.
'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an ƴan sandan jihar sun yi nasarar dakile hare-haren ƴan bindiga a wurare biyu, inda suka kubutar da mutane 18 daga hannun su.
Haka kuma, ƴan sandan sun dakile yunƙurin ƴan bindiga na sace shanu, bayan sun yi musayar wuta a kan hanyar Funtua zuwa Gusau.
Asali: Legit.ng