Kungiyar Yarbawa Ta Harzuka, Ta Fara Yamutsa Hazo kan Samar da Kotun Shari'ar Musulunci

Kungiyar Yarbawa Ta Harzuka, Ta Fara Yamutsa Hazo kan Samar da Kotun Shari'ar Musulunci

  • Wata kungiyar hadin kan Yarbawa ta yi Allah wadai da yunkurin wasu mutane na kafa kotun Shari'ar Musulunci
  • Arch. Opeoluwa George, wanda shi ne shugaban kungiyar ya ce ba za su nade hannayensu su na kallo har a kafa kotun ba
  • Ya bukaci gwamnatin jihar Oyo da ta gaggauta takawa shirin birki, domin a zaton su, zai jawo masu tashin hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Oyo - Kungiyar hadin kan Yarbawa ta duniya ta yi kakkausan suka kan shirin kafa kotun Shari’ar Musulunci a jihar Oyo da wasu ke kokarin yi.

Kungiyar, wacce ta haɗa manyan ƙungiyoyi kamar Agbekoya, Soludero, OPC, Ƙungiyar mafarauta da sauran kungiyoyi ta ce ba za ta taba amincewa ba.

Kara karanta wannan

Alkali da lauyoyi sun tsure yayin da aka fara harbe harbe ana tsaka da shari'a a kotu

Makinde
Kungiyar Yarbawa ta nemi a dakatar da shirin kafa kotun Musulunci a Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa shugaban ƙungiyar, Arch. Opeoluwa George, ya ce kafa kotun wani ƙoƙarin haifar da rikici a garin Oyo da sauran kasar Yarbawa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa, wannan abu na iya hana cigaban da ake samu a jihar da kasar Yarbawa, kuma za su yi tsayin daka wajen ganin ba a cimma manufar ba.

Batun kotun musulunci ta fusata kungiyar Yarbawa

Shafin ma'aikatar yada labarai da wayar da kai na kasa ya wallafa cewa Mista George ya ce su masu son zaman lafiya ne, amma kafa kotun zai tarwatsa shi.

Ya kara da cewa;

“Mutanen Yarbawa sun kasance masu son zaman lafiya kuma masu karɓar baki, mun gina al’adunmu da ƙa'idojinmu domin jagorantar al’umma a duniya. Yarbawa sun zama sanannu wajen karɓar addinai daban-daban da kuma zaman lafiya a duk duniya.”

A zatonsa, samar da kotun shari'ar Musulunci zai tarwatsa masu zaman lafiyar da su ke mora a halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani kan hukuncin kotu game da masarautar Kano

Kotun musulunci: Kungiyar Yarbawa ta kokawa gwamnati

Kungiyar hadin kan Yarbawa ta duniya ta bukaci gwamnatin jihar Oyo da ka da ta amince wasu mutane su samar da kotun shari'ar Musulunci a jihar.

Kungiyar ta kara da cewa;

"Ba za mu amincewa wannan shiri ba kwata-kwata, kuma muna kira ga Gwamnatin jihar Oyo da ta dakatar da shirin domin gujewa matsalar da mu ke hangowa.

Kungiyar da wasu kungiyoyi a yankin sun fusata tun bayan da wata kungiya ta bayyana aniyarta na samar da kotu shari'ar musulunci domin musulman da ke wurin.

MURIC ta yi raddi kan batun kotun Musulunci

A wani labarin, mun wallafa cewa kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC, ta bayyana rashin jin dadin ta kan gwamnatin Oyo bisa batun kotun musulunci.

Kungiyar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa a rika tayar da jijiyar wuya a kan al'amarin ba, musamman ganin yadda musulunci ya dade a yankin Yarbawa.

Kara karanta wannan

Kayayyakin miliyoyin naira sun kone bayan tashin gobara a fitacciyar kasuwa

Ta ce kamata ya yi yadda Musulmi suka yi hakuri da sauran kotuna, kowa ma ya yi hakuri, a bar musulmai su samar da kotun da za su aminta da hukuncinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.