Gwamna Ya Duba Halin da Ake ciki, Ya Yiwa Sarakuna Karin Albashi zuwa N350,000
- Gwamnatin Abia ta fara biyan karin albashi daga N250,000 zuwa N350,000 duk wata ga sarakunan gargajiya na jihar
- Gwamnatin ta shirya sake fasalin tsarin ci gaban jihar na shekaru 30 don ya yi dai dai da yanayin tattalin da ake ciki yanzu
- Gwamna Alex Otti ya dauki matakai masu tsauri kan kasuwanci a kan tituna da kuma tukin hannu daya don rage hadurra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - Gwamnatin Abia ta amince da biyan karin albashi daga N250,000 zuwa N350,000 duk wata ga sarakunan gargajiya a jihar.
Kwamishinan labarai na Abia, Okey Kanu, ya bayyana haka ranar Litinin yayin taron manema labarai kan sakamakon taron majalisar zartaswa a Umuahia.
Gwamna ya karawa sarakuna albashi
Okey Kanu ya ce shugabannin majalisar sarakunan gargajiya a matakin jiha da kananan hukumomi za su samu karin N100,000 duk wata inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kanu ya jaddada jajircewar gwamnati wajen daraja sarakunan gargajiya da kuma karfafa al’adun gargajiya na jihar.
Ya bayyana cewa gwamnati za ta sake tsara tsarin ci gaban jihar na shekaru 30 domin ya dace da halin tattalin arziki na yanzu.
Kanu ya ce an shirya kaddamar da kwamitin tattalin arziki ta jiha da za ta jagoranci aikin nan ba da jimawa ba.
“Tawagar za ta sabunta tsohon tsarin domin dacewa da tallain arzikin yanzu ta hanyar la’akari da farashin kayayyaki da ayyuka."
- Okey Kanu.
Abia ta waiwayi masu kasuwanci a kan titi
Ya ce halin da ake ciki a tattalin arzikin kasa na yanzu ya sa wajibi ne a sake wannan tsari don ya dace da halin da al’amura ke gudana yanzu.
Gwamnatin ta sake duba aikin tawagar duba tsare-tsaren jiha don tabbatar da bin ka’idoji kan kasuwanci a kan titi da tuki a kan hannu daya.
Ya ce gwamnati ta nuna damuwa kan yadda ake yin kasuwanci a kan tituna da kuma tukin hannu daya, wanda yake haifar da matsaloli.
Abin da gwamnati ta ce kan tsarin tituna
Punch ta rahoto kwamishinan watsa labaran ya ci gaba da cewa:
“Wadannan matsalolin sun zama hadari ga al'umma, kuma gwamnati ta dauki matakin tabbatar da bin ka’idoji don kaucewa hakan.
“Manyan hanyoyi da aka gina na bukatar kulawa, wanda yin kasuwanci a kan titunan ke jawo lalacewarsu da sauri."
Kwamishinan ya ce bin hannu daya a titi mai hannu biyu, ko da na gajerar tafiya ce na haddasa hadurra a lokuta da dama a jihar.
Gwamnatin ta ce ta dauki matakai masu tsauri don tabbatar da bin dokoki domin dakile wadannan dabi’u a jihar.
Gwamna ya ninka albashin sarakuna
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Inuwa Ƴahaya na jihar Gombe ya kara wa sarakunan gargajiya albashi, a cewar kwamishinan kananan hukumomi.
Gwamnan na jihar Gombe ya bukaci sarakunan su cigaba da tallafawa gwamnati wajen tabbatar da tsaro a jihar, domin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng