Gwamna Arewa Ya Ninka Wa Sarakunan Gargajiya Albashinsu a Jiharsa

Gwamna Arewa Ya Ninka Wa Sarakunan Gargajiya Albashinsu a Jiharsa

  • Gwamna Inuwa Ƴahaya na jihar Gombe ya kara wa sarakunan gargajiyar jiharsa albashi
  • Kwamishinan ƙananan hukumomin jihar, Alhaji Jalo, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Gombe
  • Ya roƙi sarakunan da su cigaba da taimakawa gwamnati a ƙoƙarin da take na tabbatar da tsaro a jihar

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amice da ƙarin albashi ga masu riƙe da muƙaman gargajiya da suka haɗa da hakimai da dagatai, kamar yadda leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan Ganawa da Nnamdi Kanu, Lauya Ya Faɗi Halin da Ya Shiga Kafin a Dawo da Shi Najeriya

Kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar, Ibrahim Dasuƙi Jalo, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Jumu'a a Gombe.

Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya
Gwamna Arewa Ya Ninka Wa Sarakunan Gargajiya Albashinsu a Jiharsa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jalo, yace: "Gwamnati ta ɗauki mataƙin ƙarin albashin ne saboda rawar da sarakuna ke takawa a jihar da kuma cika alƙawarin da gwamna ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe."

"Ƙarin albashin zai fara aiki ne daga watan Yuni, inda hakimai 165 da kuma dagatan ƙauyuka 602 zasu amfana."

"Hakimai dake mataki na 6 zasu koma zuwa mataki na 12, yayin da dagatai dake mataki na 3 zasu koma zuwa mataki na 8."

"Sannan akwai wasu kuɗin ofis na naira dubu N15,000 ga kowane hakimi a wata." inji shi.

Gwamnati zata gyara gidajen sarakuna

Dangane da lamarin gidajen sarakunan gargajiya, Kwamishinan ya faɗi cewa an tura waɗanda zasu je su duba gidajen, sannan su kawo rahoto ga gwamnati kan abinda ya dace a yi wa gidajen nasu domin gyara.

Hakanan kuma, kwamishinan ya roƙi sarakunan na gargajiya su cigaba da ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro a yankunan su.

Sannan kuma su saka ido a kan duk abinda ka iya zuwa ya dawo wanda zai iya kawo tarnatsi a zaman lafiyar yankunan su.

KARANTA ANAN: Yadda Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i Ya Cire Ɗansa Daga Makarantar Gwamnati a Sirrince

Sarakunan sun yaba wa gwamnan Gombe

A jawabinsa a madadin yan uwansa sarakunan gargajiya na jihar Gombe, Sarkin Gombe, Alhaji Abdulkadir Abubakar, yayi godiya bisa wanna abun alkairi da gwamna ya musu.

Sannan ya bayyana cewa dama sun jima suna jiran irin wannan rana da za'a ƙara musu albashinsu.

Ya kuma roƙi sarakuna da su yi amfani da wannan damar wurin taimaka wa gwamnati magance duk wani ƙalubalen tsaro a yankunansu.

A wani labarin kuma Yan Majalisa Sun Bankaɗo Wata Sabuwar Badaƙala a Rundunar Sojin Ƙasa, Zasu Fara Bincike

Majalisar wakilai ta gano wata badaƙala a rundunar sojin ƙasa ta rashin biyan ƙananan sojoji alawus ɗinsu, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Majalisar ta umarci kwamitin ta dake kula al'amuran sojojim ƙasa ya gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: