Hafsan Tsaro Ya Fadi Sinadarin Kawo Ƙarshen Ta'addanci a Najeriya
- Shugaban hafsun tsaro kasar nan, Janar Christopher Musa, ya fadi abubuwan da ke kara ta'azzara yaki da ta’addanci a Najeriya
- Ya ce talauci, yunwa, da rashin ingantattun ababen more rayuwa suna taimakawa wajen shigar da matasa a cikin kungiyoyin ta’addanci
- Janar Christopher Musa ya shawarci gwamnatin Najeriya da sauran makwabtan kasashe a kan yadda za a yi wa matsalar rubdugu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban Rundunar Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana matakan da gwamnati za ta dauke domin taimaka mata wajen yakar ta’addanci.
Ya bayyana cewa talauci, yunwa, da rashin ingantattun ababen more rayuwa suna daga cikin manyan abubuwan da ke taimakawa wajen shigar da matasa cikin kungiyoyin ta'addanci.
A cikin wata hira da Arise News, Janar Musa ya yi nuni da bukatar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da kuma na cikin gida domin samun nasarar yakar Boko Haram da sauran kungiyoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa a wasu daga cikin al’ummomin da ta’addanci ya shada su na fama da talauci da rashin wasu muhimman abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi, ruwa, da wutar lantarki.
Ta’addanci: Sojoji sun nemi tallafin gwamnati
Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa sai gwamnati ta samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasa matukar ana son a kawo karshen ta'addanci.
Janar Christopher Musa ya ce:
“Don samun mafita ta karshe a kan ta’addanci, dole ne mu samu goyon bayan gudanarwa mai kyau.
"Gudanarwa mai kyau tana da matukar muhimmanci, saboda idan muka shiga cikin wasu daga cikin wadannan al’ummomin, da yawa daga cikinsu ba su san komai game da gwamnati ba.
Idan ka tafi can, babu hanyoyi, babu ruwa, babu wutar lantarki, kuma muddin muna da talauci da yunwa, wannan shi ne abinda ake amfani da shi wajen daukar matasa cikin kungiyoyin ta’addanci.”
Sojoji suna yakar ta’addanci
Janar Musa ya kara da cewa, yana da muhimmanci a samu hadin gwiwa da kasashen makwabta, tare da maida hankali kan sarrafa iyakokin kasa domin hana shigo da makamai.
Ya ci gaba:
"Ina iya fada muku cewa a kowace mako, muna daukar matakai da yawa, amma yadda suke samun damar shigo da kayan aiki daga wasu kasashe yana kara wahalar da lamarin."
Dakarun Sojoji sun farmaki yaran Turji
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojoji sun yi nasarar kashe wasu daga cikin manyan kwamandojin ‘yan bindiga masu biyayya ga kasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji.
Mai magana da yawun rundunar, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya tabbatar da wannan nasara a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an kashe 'yan bindiga da dama.
Bello Turji ya shahara wajen jagorantar kungiyar ‘yan bindiga da ke ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yamma, musamman a jihar Zamfara, inda su ke kai hare-hare ga mazauna yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng