Mazauna Benuwai Sun Fara Tserewa daga Gidajensu da 'Yan Bindiga Suka Kashe Manomi

Mazauna Benuwai Sun Fara Tserewa daga Gidajensu da 'Yan Bindiga Suka Kashe Manomi

  • Masu garkuwa da mutane sun kashe wani manomi bayan sun karɓi kuɗin fansa daga iyalansa a garin Akor da ke Benuwai
  • Dangin manomin sun biya 'yan bindigar N5.4bn don a karbo shi, amma aka tsinci gawarsa a wurin da aka ajiye kuɗin fansar
  • Mazauna yankin Akor da wasu makotan garuruwa sun fara guduwa saboda tsoron karin hare-hare daga masu garkuwa da mutanen
  • Sai dai da aka tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Benuwai, ta ce ba ta samu wani rahoto game da wannan lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benuwai - Wasu ’yan bindiga sun kashe wani manomi, Terzungwe Shaku, a ƙauyen Akor da ke karamar hukumar Guma, jihar Benuwai.

An sace Terzungwe Shaku, wanda ke da mashaya a kasuwar Akor, a karshen shekarar 2023 kuma aka tsare shi na fiye da makonni biyu.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Kebbi da 'yan ta'addan Lakurawa suka kashe ma'aikata 4

Mazauna wasu kauyukan Benuwai sun fara tserewa daga garuruwansu saboda tsoron 'yan bindiga
'Yan bindiga sun kashe manomi a Benuwai bayan karbar kudin fansa. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun kashe manomi a Benuwai

Mazauna yankin sun ce masu garkuwar sun fara neman Naira miliyan 20, amma aka sasanta zuwa Naira miliyan 5.4, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangin Shaku sun biya kuɗin fansar da aka yarda da shi, amma daga baya an kashe shi a wurin da aka aje kuɗin.

"Abin takaici ne cewa an tsinci gawar Terzungwe Shaku a wurin da ya kamata a sake shi," in ji wani daga cikin danginsa.

An taba kai wa manomin hari

A halin yanzu, mazauna Akor da wasu ƙauyuka a Nzorov, karamar hukumar Guma, sun fara guduwa saboda tsoron karin hare-hare.

Wani mazaunin yankin ya ce an kai hari kan Terzungwe bara, amma wannan karo ’yan bindigar sun yi garkuwa da shi.

Bayan an biya kuɗin fansa a wurin da aka umurta, sai aka kashe Shaku a nan take.

'Yan sandan Benuwai ba su da labari

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi kauyuka suna yanka mutane da wuka, sun kashe rayuka

Mazaunin ya ƙara da cewa ’yan bindigar sun harbe Shaku jim kaɗan bayan danginsa sun bar wurin da aka ajiye kuɗin fansar.

Dangin sun ji harbe-harben bindiga kuma da suka koma wurin, sai suka ga gawarsa a kwance.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ta bayyana cewa ba ta da labarin abin da ya faru a halin yanzu.

Benuwai: 'Yan bindiga sun kashe mutane 30

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu gungun ’yan bindiga sun kashe akalla mutane 30 a ƙauyen Ayati da ke karamar hukumar Ukum, jihar Benue.

Wannan harin ya faru wata guda bayan wasu mahara sun kashe mazauna ƙauyen 11, wanda ya jawo zanga-zanga a lokacin.

Mazauna yankin sun ce harin ya auku a garin Ayati, hedikwatar gundumar Borikyo, inda adadin mutanen da aka kashe ya haura 30.

Cif Ayati, fitaccen ɗan siyasa, ya ɗora alhakin asarar rayukan kan gazawar shugabanni wajen dakile matsalar tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.