Tinubu Ya Fice daga Abuja, Ya Shilla zuwa Kasar Waje a Karo na 2 cikin Janairu
- Shugaba Bola Tinubu ya tafi Abu Dhabi don halartar taron ADSW na 2025, wanda ke tattauna dabarun ci gaba da tattalin arziki
- Taron shekara-shekara na ADSW da ke gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa na samar da hadin kai, da tsare-tsaren makamashi
- Tinubu zai bayyana nasarorin gwamnatinsa yayin taron tare da tattauna hanyoyin karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da UAE
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), don halartar taron ADSW na 2025.
An rahoto cewa Shugaba Tinubu ya tashi daga bangaren shugaban kasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja, da misalin karfe 6:30 na yamma.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X ta nuna cewa za a gudanar da taron ADSW na tsawon mako guda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya shilla zuwa kasar UAE
Sanarwar Bayo Onanuga ta ce:
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja ranar Asabar 11 ga watan Janairu domin halartar taron ADSW na 2025 da za a gudanar a Abu Dhabi
"Mai Martaba Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, shugaban UAE, ya gayyaci Shugaba Tinubu domin halartar taron, wanda zai gudana daga ranar 12 zuwa 18 ga Janairu."
Manyan jami’an gwamnati da suka yiwa Tinubu rakiya sun hada da shugaban ma’aikata, Femi Gbajabiamila, da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje.
Abin da taron ADSW na 2025 ya kunsa
Taron ADSW na 2025 zai tattara 'yan siyasa, manyan 'yan kasuwa da wakilan kungiyoyin farar hula daga sassa daban-daban na duniya.
Zasu tattauna dabaru da za su kawo saurin samun ci gaban duniya mai dorewa da bunkasa tattalin arziki a matakin kasa da kasa.
Taron shekara-shekarar ya kasance dandamali na duniya na tallafa wa hanyoyin samar da mafita mai dorewa ta tsawon sama da shekaru 15.
Ana jin dadin taron saboda kafa yarjejeniyoyi masu muhimmanci, hadin gwiwa na dabarun ci gaba, da samar da sababbin tsare-tsaren makamashi mai tsafta.
Tinubu zai isar da manufofin Najeriya a UAE
Shugaba Tinubu zai bayyana nasarorin gwamnatinsa da ayyukan sauye-sauye masu nufin bunkasa isasshen makamashi, kimiyya a sufuri da yadda ya inganta kiwon lafiya.
Shugaban kasar zai kuma jaddada aniyar Najeriya wajen magance matsalolin duniya ta hanyar amfani da dabaru masu dorewa da hadin gwiwa.
Baya ga halartar taron, Shugaba Tinubu zai tattauna da shugabannin UAE don kara karfafa dangantaka da tattauna bukatun kasashen biyu.
Wadannan tattaunawar na nufin samar da damarmakin hadin kai tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Tinubu zai dawo Najeriya 16 ga Janairu
Shugaba Tinubu zai yi amfani da wannan dama don kara bayyana aniyar Najeriya kan manufofin ci gaban kasa da kasa.
Ana tsammanin Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya a ranar Alhamis, 16 ga Janairu, bayan an kammala taron da ke da muhimmanci ga manufofin dorewar Najeriya.
Taron ADSW na 2025 zai taimaka wajen tabbatar da ci gaban Najeriya a matsayin jagorar ci gaba mai dorewa a matakin duniya.
Tinubu ya ziyarci sama da kasashe 15 a 2023/2024
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci sama da kasashen waje 15 tun bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023.
Haka kuma, an gano cewa Shugaba Bola Tinubu ya kwashe sama da kwanaki 96 a kasashen waje yayin wadannan tafiye-tafiyen zuwa kasar Landan, Faransa da sauransu.
Asali: Legit.ng