"Yadda su Obasanja Suka Hana Tsohon Shugaban Libiya, Gaddafi Shigo da Makamai Najeriya"

"Yadda su Obasanja Suka Hana Tsohon Shugaban Libiya, Gaddafi Shigo da Makamai Najeriya"

  • Reno Omokri ya bayyana yadda aka hana tsohon shugaban Libiya shigo da makamai cikin Najeriya a zamanin Olusegun Obasano
  • Tsohon hadimin na Goodluck Jonathan ya ce hakan da aka yi ya tabbatar da Najeriya a matsayin jagorar Afrika fiye da kasar Ghana
  • Omokri ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan yadda shugaban Burkina Faso ya je gaban shugaban kasar Ghana da bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Reno Omokri, tsohon mataimaki na musamman ga Goodluck Jonathan, ya bada labarin yadda aka hana Muammar Gaddafi shigo da makamai Najeriya.

Reno Omokri ya bada wannan labarin ne yayin da yake mayar da martani kan karya ka’idar da Shugaban Burkina Faso, Ibrahim Traoré, ya yi a Ghana.

Reno Omokri ya yi magana kan yadda shugaban Burkina Faso ya karya doka da ya je wajen shugaban Ghana da bindiga
Reno Omokri ya tuna lokacin da aka hana Gaddafi shigo da makamai Najeriya a mulkin Obassanjo. Hoto: @Oolusegun_obj, @AfricanHub_, @realFFK
Asali: Twitter

Rantsar da shugaban Ghana ta bar baya da kura

Kara karanta wannan

Hafsan tsaro ya 'gano' masu taimakon ta'addanci, ya nemi alfarmar Majalisar Dinkin Duniya

A martanin da ya wallafa a shafinsa na X, Reno Omokri ya ce Traoré ya nuna rashin girmamawa yayin da ake rantsar da shugaban Ghana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omokri ya caccaki yadda Traoré ya je wajen Shugaba Mahama alhalin akwai makami a tare da shi, inda ya kara da cewa irin wannan abu ba zai taba faruwa a Najeriya ba.

Omokri ya ce abin da ya faru ya kara tabbatarwa duniya cewa Najeriya ce ke kan gaba a jagorancin yankin da kuma tazara da ke tsakaninta da Ghana.

Yadda aka hana Gaddafi shigo da makamai Najeriya

Tsohon hadimin ya bayyana cewa sau biyu ana hana Gaddafi da 'yan rakiyarsa shigo da makamai Najeriya a lokacin mulkin Obasanjo.

Omokri ya ce lamarin farko ya faru a taron shugabannin Afrika kan yaki da zazzabin cizon sauro, wanda aka gudanar a ranar Talata, 25 ga Afrilu, 2000.

A wannan taron, Omokri ya ce ‘yan sandan Gaddafi mata sun yi kokarin shiga zauren taron da makamai, amma CSO na Obasanjo ya hana su.

Kara karanta wannan

'Magana ta fara fitowa': Hamza Al Mustapha ya fadi dalilin ganawa da El Rufa'i

"Gaddafi ya shigo Najeriya da jirgin makamai" - Omokri

Reno Omokri ya ce yunkurin shiga da makaman na biyu ya fi na farko ban tsoro, inda abin ya faru a taron Afrika da Kudancin Amurka a Abuja, a watan Nuwambar 2006.

"Gaddafi ya iso Abuja da jirage guda biyar dauke da motoci 50, wadanda ke cike da makamai, amma jami’an Najeriya suka hana shi shigowa da su.
"Jami’an Najeriya sun yi barazanar dawo da makaman zuwa cikin jiragen karkashin kulawar sojojin Najeriya, wanda hakan ya fusata Gaddafi."

- A cewar Omokri.

An hana Gaddafi amfani da makamai a Najeriya

Ana cikin hakan ne Obasanjo ya bai wa Femi Fani-Kayode shawarar warware rikicin amma da tabbacin cewa makaman ba za su shiga Abuja ba.

Duk da barazanar Muammar Gaddafi na dawowa Libya, an ce Fani-Kayode ya tsaya tsayin daka har aka mayar da makaman cikin jiragen da aka shigo da su.

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Yadda almajiri ya taso ya zama shugaban NNPCL a Najeriya

Bayan an ba Gaddafi damar shiga Abuja, jami’ansa sun yanka rago a kofar gidan da aka tanada masa sannan ya shiga.

Omokri ya ce wannan ya nuna yadda Najeriya ta kasance mai cin gashin kanta fiye da yadda Ghana ta kasa tabbatar da hakan a kan Shugaba Traoré.

Wasu kalaman Gaddafi sun fara zama gaskiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasar Libiya, Muammar Gaddafi, a shekarar 2009 ya jawo hankalin al’ummar Afrika a kan makircin kasashen Turai.

Gaddafi ya gargadi kasashen Afrika kan amincewa da kasashen Turai, inda ya yi ikirarin cewa za a dawo da cinikiyyar bayi muddiin aka goyi bayan Turawa har suka kashe shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.