Naira Biliyan 300 Ya Yi Batan Dabo tsakanin Hukumomin Kula da Harkar Mai

Naira Biliyan 300 Ya Yi Batan Dabo tsakanin Hukumomin Kula da Harkar Mai

  • Hukumomin NUPRC da NMDPRA sun kasa yin bayani kan kudade da suka kai Naira biliyan 309 da dala biliyan 2.28
  • Wani rahoto ya fallasa gazawar hukumomin wajen bin ka’idojin doka da yin aiki cikin gaskiya da tsarin tattara haraji
  • Rahoton Ofishin Mai Binciken Kudi na kasa ne ya fitar da rahoton bayan binciken asusun hukumomin tarayya biyu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Ofishin Mai Binciken Kudi na kasa ya zargi hukumomi biyu da ke kula da harkokin man fetur a Najeriya sun kasa yin bayani a kan inda N313bn su ka maƙale.

Wannan ya fito ne daga rahoton binciken kudi na baya-bayan nan da Ofishin ya fitar, inda ake zargin tauye asusun gwamnatin tarayya da rage mata kuɗin shiga da ya dace ta samu.

Kara karanta wannan

EFCC: Tsohon gwamna ya shiga matsala, kotu ta ƙwace masa sama da N200m

Fetur
Ana zargin hukumomin fetur da rashin gaskiya Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Premium Times ta ruwaito hukumomin da ake zargi sun hada da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur da Iskar Gas (NUPRC) da Hukumar Daidaita Farashin Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An binciki asusun hukumomin harkar fetur

Daga cikin kudaden da ake zargi sun bace akwai: kudaden haraji na royalties da ba a biya ba, rashin biyan tallafin jigilar mai da ake kira da bridging allowances.

Mai binciken kudi ya gano cewa $1.65bn ne kudaden haraji na royalties da Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya kamata ya biya ga asusun CBN da DPR.

Sai dai, DPR ta karbi $1.4bn kawai daga cikin $1.65bn da ake tsammanin ta karba, wanda hakan ya bar gibin $254bn a matsayin kudaden haraji da ba a biya ba na wannan lokacin.

An bankaɗo gazawar hukumomin fetur

Rahoton ya bayyana yadda hukumomin suka kasa yin aiki yadda ya kamata tare da rashin bin ka’idoji na doka wajen mika kuɗaɗen da ya dace su shiga asusun gwamnati. An gano cewa a shekarar 2021, hukumomin NUPRC da NMDPRA ba su yi bayanin yadda aka kashe Naira biliyan 309 da $2.28bn da su ka samu a wancan lokaci ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware biliyoyin Naira kan jiragen shugaban kasa a 2025

Hukumomin man fetur da ake zargi da almundahana

An kafa wadannan hukumomi biyu a watan Agustan 2021 bayan sanya hannu kan dokar Man fetur ta PIA da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

Gbenga Komolafe shi ne shugaban farko na NUPRC tun daga watan Satumba 2021 kuma har yanzu yana rike da mukamin, yayin da Farouk Ahmed ya kasance shugaban NMDPR.

Ana zargin kamfanin mai fetur da almundahana

A wani labarin, mun ruwaito cewa rahoton Ofishin Mai Bincike na Kasa ya zargi Kamfanin Man Fetur na NNPCLda zambar kudade da suka kai Naira biliyan 514.

Wannan zargi ya fito ne daga binciken da aka gudanar kan asusun kamfanin na shekarar 2021, wanda aka buga a watan Nuwamba 2024, kuma aka saki kwanan nan.

Rahoton ya bayyana cewa NNPCL ta karkatar da kudade da kuma amfani da wasu daga cikin kudaden da aka ware don gudanar da ayyuka ba bisa ka'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.