'Mutum 3927 Za a Ɗauka': Ƴan Najeriya da Suka Nemi Aikin Kwastam Sun Haura 573, 000

'Mutum 3927 Za a Ɗauka': Ƴan Najeriya da Suka Nemi Aikin Kwastam Sun Haura 573, 000

  • Hukumar Kwastam ta ce sama da mutane 573,000 suka nemi guraben aiki 3,927 a cikin mako guda da bude shafin daukar aikin
  • Kakakin jami'an kwastam, Abdullahi Maiwada ya bayyana cewa wadanda suka nemi aikin da takardun digiri da HND sun haura 27,000
  • Hukumar tarayyar za ta tantance wadanda suka nemi aikin don tabbatar da gaskiya da adalci wajen daukar waɗanda suka cancanta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa kimanin mutane 573,519 suka nemi guraben aiki 3,927 da aka buɗe na zangon 2024/2025.

Idan za a tuna, Ministan Kuɗi, Olawale Edun, ya tabbatar da amincewar gwamnatin tarayya na ɗaukar ma’aikata 3,927 a hukumar Kwastam.

Hukumar Kwastam ta yi bayani game da yawan 'yan Najeriya da suka nemi gurbin aiki a NCS
Sama da mutane 730,000 suka nemi aiki a hukumar Kwastam ta Najeriya. Hoto: @CustomsNG
Asali: Facebook

Mutane 573,519 sun nemi aikin Kwastam

Abdullahi Maiwada, jami’in hulɗa da jama’a na NCS, ya bayyana cewa mutane 573,519 suka cike fam din neman aikin da aka fitar, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi magana kan gwamnan da ake tsoron zai sauya sheka zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce akwai rukuni biyu na waɗanda suka nemi guraben: Ma'aikata masu tallafawa, waɗanda ƙwararru ne da kuma jami'an ayyukan gama gari.

Jami'in ya ce mutane 349,218 ne suka nemi aiki a karkashin matakin sufuritanda (ayyukan gama gari).

A matakin sufuritanda (jami'ai masu tallafawa), akwai mutane 27,722 da suka nemi aikin ta hanyar gabatar da takardunsu na HND da kuma digiri.

Masu Digiri, ND, NCE da SSCE sun nemi aikin

A matakin sufeta, an samu mutane 115, 634 da suka nemi aiki a bangaren gama gari da 12,952 a bangaren jami'ai masu tallafawa.

Jaridar Vangaurd ta rahoto Abdullahi Maiwada ya ce wadannan sun nemi aikin ne ta hanyar amfani da takardun NCE ko ND.

A matakin jami'in CS kuwa, an samu waɗanda suke da takardar sakandare a bangare biyu: masu kiredit biyar da suka ci lissafi da Turanci da waɗanda ba su ci darusan biyu ba.

Kara karanta wannan

EFCC: Wasu ma'aikatan gwamnatin tarayya sun shiga matsala, an kore su daga aiki

A bangaren jami'an ayyukan gama gari, mutane mutane 153,593 suka nemi aikin yayin da wasu 14,400 suka nemi aikin a bangaren jami'ai masu tallafawa.

Kwastam za ta yi adalci wajen daukar aikin

Abdullahi Maiwada ya bayyana cewa yawan mutanen da suka cike fom din neman aikin ya nuna ƙarfin gwiwar matasa na burin shiga hukumar kwastam.

Hukumar ta sanar da cewa za ta ci gaba da tantance waɗanda suka nemi aikin don tabbatar da cewa an zabi wadanda suka cancanta cikin gaskiya da adalci.

Hukumar Kwastam ta fara daukar aiki

Tun da fari, mun ruwaito cewa hukumar Kwastam ta Najeriya ta bude shafinta domin daukar ma'aikata a zangon shekarar 2024/2025.

Yayin da hukumar ta ce neman aikin kyauta ce, ta kuma ce za a fara cike neman aiki daga ranar 27 ga Disamba, 2024 zuwa ranar 2 ga Janairu, 2025.

Sai dai a lokacin da aka bude shafin, an samu tangarda a shafin hukumar, inda mutane da dama suka yi korafi na rashin samun damar cike fom din.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.