Daukar aiki: Hukumar Kwastam ta zubar da wadanda basu can canta ba

Daukar aiki: Hukumar Kwastam ta zubar da wadanda basu can canta ba

-Mutum 524,315 ne suka nemi aiki da Hukumar Yaki da fasa Kwabri

-Hukumar Yaki da fasa kwabri zata daukin mutum 3,200 ne kacal, cikin 524,315 da suka nemi aikin

- Wadanda sukayi nasara karon farko, za a gayyace su jarabawa

Hukumar yaki da fasa kwabri ta zubar da masu neman aiki da ita da basu da muhimman abubuwan da ake nema.

Jami'in hulda da zama'a na hukumar Mr.Joseph Attah ne ya bayyanawa yan jarida hakan a rananr Alhamis 13 ga watan Yuni, 2019.

Mutane 524,315 suka nemi aiki da hukumar wacce ke bukatar mutum 3,200 kacal.

KARANTA WANNAN: Matasan Ibo sun bayar da sunan wanda suke so Buhari ya nada SGF

Attah ya bayyana cewa an fara zubar da wadanda basu dace da aikin ba, inda ya bayyana cewa hukumar na bukatar ma'aikata masu kwarewa a wasu fannoni ba wai kowa da kowa ne ake bukata ba.

"Wanna aikin kwararru kawai ake nema ba wai na gama gari bane. Muna daukar kowa da kowa idan zamuyi daukar aikin gama gari ba tare da la'akari da abunda mutum ya karanta ba"

Attah ya bayyana cewa har yanzu de ana tan tancewa kuma da zarar an gama za a gayyaci wadanda sunayen su ya fita zuwa jarabawa ta nambobin wayarsu.

Ya bayyana cewa za a gudanar da jarabawan a babban birnin jihar da kowa yake.

"Alal misali idan kana Borno to zaka rubuta jarabawarka a Maiduguri, idan kana Kogi to zakayi jarabawarka a Lokoja, idan kana Zamfara zakayi a Gusau idan kana Rivers to zakayi a Portharcourt, haka duk sauran jihohin."

Ya bada tabbacin cewa za a gudanar da daukar aikin cikin yadda da amana, yana mai cewa duk wanda ya hada abubuwan da ake so to za a gayyace shi jarabawar.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta;

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa ta musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel