Kwastam: An fitar da cikakken sunayen sabbin ma'aikata da za a ɗauka aiki a 2021

Kwastam: An fitar da cikakken sunayen sabbin ma'aikata da za a ɗauka aiki a 2021

Hukumar Hana Fasakwabri ta Najeriya, Kwastam, ta fitar da sakamakon karshe na wadanda suke neman shiga aiki a hukumar a shekarar 2021.

A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, ta bukaci wadanda aka fitar da sunayensu da su tafi zuwa ofishinta da ke tsohuwar sakatariyar tarayya da ke Area 1, Garki Abuja daga ranar 8 ga watan Nuwamba zuwa 7 ga watan Disamban 2021 don gabatar da takardunsu.

Jerin Sunaye: An fitar da sunayen sabbin ma'aikatan Kwastam da za a ɗauka aiki a 2021
An fitar da sunayen sabbin ma'aikatan Kwastam da za a ɗauka aiki a 2021. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ana sa ran wadanda suka yi nasarar samun aikin su taho da wadannan abubuwan:

  1. Satikifet dinsu na ainihi
  2. Takardan shaidan garin da suka fito
  3. Takardan shaidan ranar haihuwa
  4. Su taho da fotocopi (4) na takardun da aka bukata a sama
  5. Hoton na fasfo guda hudu (4)

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An bindige wani mutum a kotu yayin da ya yi ƙoƙarin tseratar da fursuna

Ga dai cikaken jerin sunayen wadanda suka yi nasarar samun aikin a nan kasa

Latsa nan domin ganin jerin sunayen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel