Masu Ritaya: An Gano Miliyoyin Naira da Gwamnati Za Ta Kashewa Manyan Jami'an Soji

Masu Ritaya: An Gano Miliyoyin Naira da Gwamnati Za Ta Kashewa Manyan Jami'an Soji

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da alawus na ritaya ga shugabannin soji, wanda ya haɗa da ganin likitocin waje da motocin alfarma
  • Duk da cewa alawus din manyan Janarori ya bambanta da na Laftanar amma dai kowanensu zai samu alawus mai tsoka lokacin ritaya
  • Likitoci sun nuna adawa kan ba sojojin alawus na fita waje neman lafiya, suna ganin akwai bukatar inganta tsarin lafiya a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da ba da alawus na ritaya ga shugabannin sojoji da janarori, wanda ya haɗa da $20,000 na neman lafiya a waje.

Haka kuma, za a samar da motocin sulke, kayan aiki, masu hidima da sauran kayayyakin alatu ga shugabannin sojoji masu ritaya.

Rahoto ya yi bayanin irin sha tara ta arziki da aka shiryawa shugabannin soji masu ritaya
Likitoci sun yi adawa da tafiyar sojoji waje neman lafiya bayan ritaya. Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Tinubu ya amince da alawus ga sojoji masu ritaya

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Bello Turji, sojoji sun kashe ɗan ta'addan da aka daɗe ana nema

Kungiyoyin likitoci na Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu game da wannan alawus, suna mai cewa bai dace sojojin su je waje neman magani ba, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin alawus din yana cikin wani kundin ayyukan jami'an soja, wanda shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 14 ga Disamba 2024.

A cikin wannan kundin, babban kwamandan tsaron kasa da sauran shugabannin sojoji suna da damar samun motar sulke ko makamancinta a matsayin alawus.

Za a rika canja masu motar bayan shekaru hudu, kuma sojoji za su kula da gyara da kulawa da ita. Haka kuma akwai mota kirar Peugeot 508 da za a kara masu da ita.

Manyan sojojoji za su samu alawus na $20,000

Shugabannin soji da suka yi ritaya za su samu wasu alawus na jin dadin rayuwa, ciki har da ma'aikatan gida da masu tsaron gidansu bayan ritaya.

Idan sojan Laftanal Janar ne, zai samu alawus na dala 20,000 a kowace shekara domin fita kasar waje neman magani.

Kara karanta wannan

An ware biliyoyi domin yin hidima ga Akpabio, Barau da sauran shugaban majalisa

Zasu samu mataimaki na musamman, direbobi guda uku da kuma mai tsaron lafiya, wanda za a samar da su bisa bukatar sashen soja.

Manyan sojoji za su rike bindigogi bayan ritaya

Har ila yau, kowanne daga cikin shugabannin soja da zai yi ritaya zai samu ma'aikatan gida guda biyar, ciki har da masu dafa abinci da masu kula da gidan.

Wannan kundin ya bayyana cewa duk shugabannin soja masu ritaya za su ci gaba da amfani da bindigoginsu amma za a mayarwa rundunar soji idan sun mutu.

Ga manjan jami'ai sirinsu Laftanar Janar da makamantansu, za su samu motoci biyu kirar Hilux, Toyota Land Cruiser, direbobi, masu tsaron gida da masu dafa abinci.

Alawus na Manjo Janar da Birgediya Janar

Gwamnatin tarayya ta kuma amince da alawus na $15,000 ga Manjo Janar domin neman magani a waje a kowace shekara da motar Toyota Land Cruiser, masu dafa abinci, direba, da masu tsaron gida guda biyu.

Kara karanta wannan

'Tinubu bai dace da Najeriya ba': Hadimin Osinbajo ya fadi mai nagarta da zai kawo sauyi

Sauran manyan jami'an soja, irin su Birgediya Janar (mai anini daya) za su samu alawus na $10,000 na neman lafiya a kowace shekara, tare da motar Toyota Camry ko makamancin haka.

Shugaban kungiyar likitoci ta NMA, Farfesa Bala Audu, ya nuna damuwarsa kan yadda ake bada alawus ga sojojin don su fita waje neman magani.

Farfesa Bala ya ce akwai bukatar ayi amfani da wadannan kudade da aka ware domin inganta tsarin lafiyar Najeriya ko don ci gaban kasar.

Za a ginawa sojoji gidaje bayan ritaya

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojin Najeriya ta kammala shirin gina gidaje ga sojojin bakin daga don samun wurin zama bayan ritaya ko nakasa.

Tsarin ya hada da ninka kudin inshorar sojoji, don inganta yanayin aikin tsaro da kuma ba sojojin kwarin guiwar sadaukar da rayuwarsu a yiwa kasa hidima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.