Sojoji da Suka yi Ritaya Sun Toshe Hedkwatar Tsaro kan Alawus da Ba a Biya su ba

Sojoji da Suka yi Ritaya Sun Toshe Hedkwatar Tsaro kan Alawus da Ba a Biya su ba

  • Sojojin Najeriya da suka yi ritaya sun mamaye kofar shiga hedkwatar tsaro Najeriya dake Abuja kan rike musu alawus da aka yi
  • Kamar yadda fusattatun sojin suka bayyana, ba za su tafi ba har sai Minista Bashir Magashi ya biya musu bukatunsu
  • Sun koka da yadda shugaba Buhari ya amince a biya su amma ministan ya nuna musu rashin tausayi da kulawa ya rike musu kudadensu

FCT, Abuja - Wasu jami’an soji da suka yi ritaya a ranar Litinin jurewa ruwan sama da aka yi a safiyar don gudanar da zanga-zangar kashi na 3 a hedikwatar ma’aikatar tsaro da ke Abuja.

Masu zanga-zangar sun yi korafi kan rashin biyansu alawus din tsaro da aka rike musu, da sauransu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sheke Manoma 3, Sun yi Garkuwa da Wasu 22

Fusatttun masu zanga-zangar tare da wasu ‘yan uwan ​​ma’aikatan da suka mutu, sun kare hanyar shiga ma’aikatar da ke gidan Ship House da ke kan titin Olusegun Obasanjo a babban birnin tarayya.

Tsofaffin sojojin da ke karkashin kungiyar Ma'aikatan Sojin Najeriya da suka yi ritaya sun zargi Ministan Tsaro, Maj.-Gen. Bashir Magashi (Mai Ritaya), da rashin kulawa da halin da suke ciki.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a yayin zanga-zangar, kakakin CVV, Abiodun Durowaiye-Herberts, ya sha alwashin ba za su bar kofar shiga ma’aikatar ba har sai an biya musu bukatunsu.

Ya ce tuni suka shirya yin bacci har dare idan lamarin ya tabbata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Muna nan tare da matanmu da ‘ya’yanmu, da kuma matan wadanda suka mutu, wadanda wasunsu suka mutu a yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram. Za mu kwana a nan har sai Ministan Tsaro, Magashi ya amsa bukatunmu."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Na Fama Da Matsanancin Yunwa Ta Yadda Basa La'akari Da Addinansu A Zaben 2023 - Keyamo

A nasa bangaren, Sakataren RMNAF na kasa, Roy Okhidievbie, wanda ya bayyana cewa zanga-zangar ta neman a biya su alawus na tsaro da gwamnatin tarayya ta rike musu ce..

Ya zargi Ministan da kin biyan alawus din duk da amincewar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

“Mun yi ganawa da Ministan Tsaro, Magashi, amma bisa dukkan alamu ya kasance mai taurin kai, rashin tausayi, kuma ba ya cikin damuwa game da korafe-korafen jami’an soja da suka yi ritaya, domin bai taba biyan ko nuna sha’awa ko damuwa na biyan wadannan alawus-alawus ba."

- Yace.

"Abin sha'awa shine, gwamnatin shugaba Buhari ta amince da biyan wannan alawus, amma Magashi ya ki ya biya."

- In ji Okhidievbie.

Borno: Zulum Ya Sanar da Abun Mamakin da Ya Faru da 'Yan Ta'adda Wanda Ba a Taba ba a Duniya

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, yace sama da mambobin Boko Haram da ISWAP 90,000 ne suka mika ga hukuma cikin shekara daya.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka

Gwamnan yayin da yake jawabi a taron majalisar dinkin duniya karo na 77 da aka yi a New York, yace ‘yan ta’adda da kansu suka dinga mika wuya wurin sojoji, jaridar TheCable ta rahoto hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel