An Shiga Tashin Hankali a Borno, 'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojojin Najeriya

An Shiga Tashin Hankali a Borno, 'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojojin Najeriya

  • An rahoto cewa mayakan ISWAP sun kashe sojoji da dama a harin da suka kai sansanin soja na Sabon Gari da ke jihar Borno
  • Hedikwatar tsaro ta tabbatar da harin da 'yan ta'addan suka kai wanda ya janyo konewar sansanin da lalacewar motocin sojojin
  • Tun daga 2009, rikicin Boko Haram da ISWAP ya halaka mutane 40,000 da raba mutane miliyan biyu daga gidajensu a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Wasu ‘yan ta’adda da ke da alaƙa da kungiyar IS sun kashe sojoji shida a harin da suka kai kan sansanin soja a Arewa Maso Gabas.

An ce mayakan ISWAP sun kai hari kan sansanin sojoji na Sabon Gari, da ke Damboa, jihar Borno ne da Asubah a saman motocin yaki da babura.

Hedikwatar tsaro ta yi magana kan harin da ISWAP ta kai sansanin sojoji a Borno
Mayakan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya da dama a harin da suka kai kan sansanin soji na Borno. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Mayakan ISWAP sun kashe sojoji a Borno

Kara karanta wannan

Barazanar tashin bam: Gwamnatin Neja ta aika da muhimmin gargadi ga manoma

Ana zargin mayakan sun banka wa sansanin sojojin da motocinsu wuta, kamar yadda rahoton jaridar AP ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun rasa sojoji shida a harin ISWAP kan sansaninmu bayan artabu mai tsanani,” a cewar wani jami’in soja.

Ana zargin jiragen yaki daga Maiduguri sun kai hari kan ‘yan ta’addan yayin da suke guduwa daga wurin.

Hedikwatar tsaro ta tabbatar da farmakin

Wani jami'in soja ya ce:

“Farmakar 'yan ta'addan ta sama ya janyo mutuwar mayakan, lalata motocinsu da makamai."

Kakakin hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar da harin ga Channels TV amma bai bayyana adadin sojojin da suka mutu ba.

“Mun tabbatar da cewa an samu cikas wajen ayyukan sojoji a yankin. Za a gudanar da bincike domin gano abin da ya faru."

- Manjo Janar Buba.

Arewa na fuskantar hare-hare tun 2009

Tun daga 2009, Arewacin Najeriya ke fama da hare-haren kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu aikata miyagun laifuffuka.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Bello Turji, sojoji sun kashe ɗan ta'addan da aka daɗe ana nema

Hare-haren 'yan ta'addan sun jawo mutuwar mutane sama da 40,000 kuma suka raba sama da mutane miliyan biyu daga gidajensu.

A watan Nuwamba, an kashe sojoji biyar kuma 10 sun ji rauni yayin da ISWAP ta kai hari kan sansanin sojoji a Kareto kusa da iyakar Nijar.

Borno: Sojojin sama sun farmaki ISWAP

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ƙarƙashin Operation Hadin Kai ta kai hare-hare kan ƴan ta’addan ISWAP da suka kai wa sojoji hari a Damboa.

Majiyoyin leƙen asiri sun tabbatar da cewa ƴan ta’addan sun kashe sojoji biyar kafin su koma yankin Timbuktu Triangle.

Da sojojojin ke mayar da martani, jiragen NAF sun gano 'yan ta'addan suna ɓoye ƙarƙashin bishiyoyi a Farin Ruwa, sansanin ISWAP a Timbuktu Triangle.

An ce wannan binciken ne ya ba sojojin saman damar sakin ruwan bama bamai kan sansanin 'yan ta'addan wanda ya jawo aka kashe miyagun da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.