Bidiyon da Ake Zargin Ya Jawo Aka Dakatar da Jaruma Samha M Inuwa daga Kannywood

Bidiyon da Ake Zargin Ya Jawo Aka Dakatar da Jaruma Samha M Inuwa daga Kannywood

  • Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa, saboda wallafa hotuna da bidiyon batsa
  • Hukumar ta bayyana cewa an sha yiwa jarumar gargadi kan shigar banza, amma ta ki ji, don haka aka dakatar da ita na shekara guda
  • Masoyan jarumar sun nuna rashin jin dadi kan dakatarwar, yayin da suka nuna mata kuskuren da ta yi a wannan bidiyo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - A jiya Asabar, 4 ga watan Janairun 2025, hukumar tace finafinai da dab'i ta jihar Kano karkashin Abba El-Mustapha ta dakatar da Samha M Inuwa.

Samha M Inuwa, jaruma ce da ke tashe a masana'antar Kannywood musamman ma a bangaren bidiyon wakoki da kuma shafukan sada zumunta.

Masu kallon finafinan Hausa sun yi Allah wadai da shigar da jaruma Samha M Inuwa ta yi.
An ga wani bidiyo da ake zargin shi ne silar dakatar da jaruma Samha M Inuwa daga Kannywood. Hoto: mutan_kannywood
Asali: Instagram

Matashiya: An kori Samha daga Kannywood

Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar tace finafinai ta Kano ta sanar da cewa ta kori jaruma Samha M Inuwa ne saboda wallafa hotuna, bidiyo da kalamai na batsa.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood Radeeya Jibril ta yi aure, ta lissafa mutane 7 da suka taimaka mata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar da jami'in watsa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, an ji cewa:

"Hukumar tace finafinan ta dakatar da Samha M. Inuwa daga fitowa a finafinai na tsawon shekara daya saboda bayyana tsiraicinta a bidiyo da kuma samun korafe-korafe a kanta."

Hukumar ta kuma ce an sha yiwa jarumar gargadi kan yadda ta ke yin shigar banza da ke nuna tsiraicinta da kuma furta kalaman batsa a bidiyon da take wallafa a intanet.

Bidiyon da ake zargin ya jawowa Samha matsala

Legit Hausa ta ci karo da wani bidiyon da ake zargin shi ne ya jawowa jaruma Samha M. Inuwa matsala, wanda ya kai ga hukumar ta yanke shawarar dakatar da ita.

A cikin bidiyon wanda aka wallafa a shafin mutan_kannywood na Instangram, an ga jaruma Samha cikin shigar kaya ta 'biri da wando' da kuma hular sanyi ta gay a kanta.

Kara karanta wannan

Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da jarumar Kannywood, an fadi dalili

Sai dai kayan sun dame jikinta, ta yadda ake iya ganin tsarin zubin jikinta a wani yanayi da wasu ke cewa 'ya na daga hankalin mutame, musamman maza.'

Abin da mutane suka ce kan bidiyon Samha

A zantawarmu da wani masoyin jarumar a nan Kaduna, Al-Ameen Ibrahim, ya ce ya yi takaicin yadda jarumar ta yi wannan shiga har ta watsa a intanet.

"Gaskiya banji dadi ba, saboda ni masoyinta ne tun daga lokacin da take fitowa a wakoki. Mu masoyanta ba mu ji dadin shigar da ta yi ba.
"Amma duk da haka, ba mu ji dadin dakatar da ita da aka yi ba, saboda akwai jaruman da su ma suna yin makamanciyar wannan shiga, ba a dakatar da su ba."

- A cewar Al-ameen Ibrahim.

Da muka leka Instagram, mun zakulo kadan daga ra'ayoyin mutane:

comrd_alamin_mustapha:

"Iyayenmu sun yi kokari sosai wajen bamu tarbiyya. Allah ya saka musu da alkhairi."

Kara karanta wannan

Rahama Sadau ta faɗi sunan wanda ya kama hannunta, ya shigo da ita Kannywood

muzammil_aliyu_shari_ah:

"Ai dama kin fito ba kayan a jikinki kamar zai fi."

abdul__famous:

"Sai an ce musu karuwai su kama kuka an yi musu kazafi."

sir___namadi:

"Kawai ki fito ba kayan mana, Allah ya shirya mu baki daya."

princeabulabdallah:

"Wai dan Allah ku dole se kun tayarwa al'ummar Annabi hankali?"

Jarumar Kannywood Radeeya ta yi aure

A wani labarin, mun ruwaito cewa jarumar Kannywood, Radeeya Jibril, ta yi aure tana mai godiya ga Allah da ya nuna mata wannan rana.

Radeeya ta bayyana cewa ta bar Kannywood lafiya kamar yadda ta shigo lafiya, tare da gode wa wasu manyan 'yan masana’antar da suka ba ta gudunmawa sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.