Ba da Mu Ba: ’Yan Najeriya Sun Kadu da Ganin Makarantar Firamaren da Ake Sayar da Fom N2m a Legas
- A kintace, Charterhouse Lagos na daga cikin makarantun firamare mafi tsada a Najeriya, inda labarin kudaden makarantar ya sake bayyana
- Shafin yanar gizon Charterhouse Lagos ya bayyana cewa, kudin rajista ga sababbin dalibai yana kai Naira miliyan 2
- Legit.ng ta tattara lissafin kudaden makarantar da suka kai miliyoyi a tsakanin ajin firamare da sakandare a makarantar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Legas - Charterhouse Lagos ta zama abin tattaunawa bayan labarin kudaden da ake biya a makarantar ya sake bayyana a kafafen sada zumunta.
Charterhouse Lagos ce makarantar farko ta Biritaniya a Yammacin Afirka kuma tana cikin kadarorin dangin Charterhouse mai daraja na makarantu.
A cewar bayanin da ke shafin yanar gizon makarantar, kudin rajista kadai ban da kudin zango ga sabon dalibi a Charterhouse Lagos yana N2 miliyan.
Abin da 'yan Najeriya ke fadi a baya
A watan Afrilun 2024, makarantar ta fuskanci suka saboda zunzurutun kudaden da take karanta, wanda aka ce yakan kai N42m a kowace shekara, tare da kudin rajista wanda ba zai gaza N2m.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Charterhouse Lagos, wanda yake a yankin Lekki na birnin Ikko, an danganta ta da kasancewa mafi tsada a jihar, ko kuma mafi tsada a Najeriya.
Legit.ng ta lura cewa kudaden makarantar da dalibai ke biya sun bambanta bisa ga ajinsu.
Yayin da yawancin makarantun Najeriya ke bayyana ajinsu ta hanyar “primary” ko ajin firamare, Charterhouse Lagos na amfani da kalmar “Year” don bambanta ajujuwa.
Kudaden Charterhouse Lagos na Year 1 zuwa Year 9
Kudin makarantar na shekara-shekara ga dalibai na Year 1 da Year 2 ya kai N16.1m, yayin da na Year 3 da Year 4 ya kai N17.15m. Daliban Year 5 da 6 na biyan N18.2m na kudin makaranta.
Kudaden makarantar dalibai na sakandare, wanda ya hada da Years 7 da 8, shi ne N21.7m, yayin da kudin Year 9 yake kan N24m.
Charterhouse Lagos ta bayyana kudaden dakunan kwana
Makarantar na da tsarin dakunan kwanan dalibai kashe biyu, wadanda suka hada da dakunan kwana na mako da dakunan kwana na cikakken lokaci, kowanne da farashinsa daban.
A cewar shafin yanar gizon makarantar, dakunan kwana na mako suna kai N5m, yayin da dakunan kwana na cikakken lokaci suke kan N7m.
A bangare guda, ‘yan Najeriya sun kalubalanci tsadar kudaden makarantar da Charterhouse Lagos ke tatsa a hannun iyaye, yayin da bidiyon makarantar ya yadu a yanar gizo.
Abin da 'yan Najeriya ke cewa yanzu
Muhawara ce ta barke a ranar Alhamis, 2 ga Janairu, 2025, bayan an yada wani bidiyo a kafar X. Ga kadan daga bin da jama’a ke cewa mun tattaro muku:
@OyinAtiBode:
“Har yanzu dai ya yi tsada sosai.”
@GladysGodwin15:
“Inda suke ci gaba da wahalar da kansu har su mutuwa?”
@Danscojack:
“Tatsar 'yan Najeriya da kudi kamar yadda aka saba. Ire o.”
@OAAdeniji:
“Babu wata hanya da zai yiwu wani a Najeriya da ke samun Naira, zai biya N42 miliyan a kowace shekara ga dalibin sakandare, ko da menene ake koya masa. Wannan ya fi tsada ma tsada.”
Makarantun sakandare mafi tsada a Najeriya
A baya, mun tattaro muku rahoto kan adadin makarantu mafi tsada a Najeriya, wadanda da yawansu mallakin 'yan kasar waje ne.
Ilimi na daya daga abin da 'yan Najeriya ke kashe kudadensu a kai, domin tabbatar da sun ba da tarbiya mafi tsarki.
Sai dai, makarantun kan tatsi kudade masu tsoka a hannun jama'a don tabbatar da an ba da ilimi mai inganci.
Asali: Legit.ng