Asalin Abin da Ya Jawo Ma’aikata 1000 Suka Bar Bankin CBN Lokaci Guda Ya Fito

Asalin Abin da Ya Jawo Ma’aikata 1000 Suka Bar Bankin CBN Lokaci Guda Ya Fito

  • Babban bankin Najeriya ya yi wa majalisar wakilan tarayya bayanin kawo tsarin da ya jawo sallamar ma’aikata
  • Olayemi Micheal Cardoso ya tura mataimakin darekta wanda ya ce babu wanda aka tilastawa barin aikin bankin
  • Wakilin gwamnan babban bankin Najeriya ya ce ma’aikata ne suka nemi su yi murabus don haka aka bude masu kofa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya ya yi karin bayani game da wasu ma’aikatan da suka bar aiki kwanan nan.

Gwamnan babban bankin kasar, Olayemi Micheal Cardoso ya yi bayani da ya warware zargin da ake yi na fatattakar ma’aikata.

Bankin CBN
Bankin CBN ya ce babu wanda aka tursasawa barin aiki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Meyasa ma'aikata rututu suka bar bankin CBN?

Jaridar The Guardian ta ce Olayemi Micheal Cardoso ya ce mutanen da suka bar aiki sun yi hakan ne saboda radin kansu ba kowa ba.

Kara karanta wannan

"An shiga wahala bayan zaben Tinubu," Sanatan APC ya fadi manufar gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan bankin ya bayyana a gaban wani kwamiti da Hon. Usman Kumo yake jagoranta domin a binciki lamarin a majalisar wakilai.

Bala Bello wanda mataimakin darekta ne a bankin ya wakilci Olayemi Micheal Cardoso domin yi wa ‘yan majalisar tarayya bayani.

Majalisa ta na binciken korar ma'aikatan CBN

Majalisar tarayya ta dage sai ta gano abin da ya jawo ma’aikata da-dama suka bar CBN.

Mista Bala Bello ya kuma shaidawa kwamitin cewa sai da aka biya kowane ma’aikacin hakkinsa kafin ya yi sallama da bankin.

A rahoton The Cable, an ji jami’in ya na yi wa majalisa bayanin yadda aka kawo tsarin sallamar domin a inganta aikin bankin CBN.

CBN ya ce ganin dama ya sa aka yi murabus

"Babu wanda aka matsawa ya tafi. Sam babu wanda aka tursasa ya bar aiki. "Tsantsar ganin dama ce. An samu wannan ne saboda bukatar mafi akasarin jama’a.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kalaman Peter Obi sun yi wa APC zafi, ta zarge shi da son tunzura jama'a

"Kamar yadda na fada na zo da wakili daga bangaren ma’aikatan domin ya fada a nan."

- Bala Bello

A gaban ‘yan majalisar ne ya ce ba a CBN aka fara ganin ma’aikata sun yi murabus ba.

Shi kuwa Hon. Kumo, ya sha alwashin cewa kwamitinsa zai yi wa kowane bangare a adalci a karshen binciken da suke gudanarwa ba.

Majalisar ta saurari shugaban bankin domin jin manufar sallamar ma’aikata watanni bayan an maida wasu ofisoshinsa zuwa Legas.

Bankin CBN ya na ta korar darektoci

A shekarar da gabata, an rahoto cewa a lokaci daya, bankin CBN ya kori daraktoci bakwai da suka yi aiki da Mista Godwin Emefiele.

Bayanai sun nuna babban bankin na shirin ƙara korar ƙarin wasu daraktoci 12. Lamarin ya haddasa sukar Yemi Michael Cordoso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng