Ma'aikata da Malama Sun Rufe Dukkanin Manyan Makarantu a Bauchi, Sun Fadi Dalili

Ma'aikata da Malama Sun Rufe Dukkanin Manyan Makarantu a Bauchi, Sun Fadi Dalili

  • Malamai da ma'aikata a Bauchi sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani tare da rufe dukkanin manyan makarantun jihar
  • Karkashin JAC, malamai da ma'aikatan manyan makarantun sun shiga yajin aikin ne kan rashin aiwatar da sabon tsarin albashi
  • JAC ta zargi gwamnatin jihar Bauchi da kin fara aiwatar da tsarin albashi na CONPCASS da CONTEDISS da kuma yi masu barazana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Kwamitin JAC na kungiyoyin malamai da ma'aikatan manyan makarantun Bauchi ya sanar da tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Alhamis.

Yajin aikin wani bangare ne na kokarin JAC wajen tabbatar da biyan sabon tsarin albashi na CONPCASS da CONTEDISS ga malamai da ma'aikatan ilimi.

Kungiyarf JAC ta bayyana dalilin ma'aikata da malaman manyan makarantu na shiga yajin aiki a Bauchi
Ma'aikata da malaman manyan makarantu sun gargadi gwamna yayin da suka shiga yajin aiki. Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Facebook

Malamai da ma'aikata sun rufe makarantun Bauchi

Manyan makarantu da abin ya shafa sun hada da kwalejin Abubakar Tatari Ali, da kwalejin ilimi ta Adamu Tafawa Balewa da ke Kangere, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kalaman Peter Obi sun yi wa APC zafi, ta zarge shi da son tunzura jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da kwalejin ilimi ta A.D Rufai da ke Misau; kwalejin ilimi ta Aminu Saleh da ke Azare da kwalejin noma ta jihar da ke kwaryar Bauchi.

Har ila yau, kwalejin kiwon lafiya da fasaha ta Bill and Melinda Gates da ke Ningi, na cikin jerin cibiyoyin da abin ya shafa.

Dalilin malamai, ma'aikata na shiga yajin aiki

A wata sanarwa da suka fitar ga manema labarai a Bauchi ranar Juma’a, shugaban JAC, Abubakar Ahmed, ya bayyana dalilan yajin aikin.

Ahmed ya nuna takaici kan yadda wakilan gwamnati suka yi watsi da bukatun kungiyar tare da amfani da dabaru na jan kafa.

Ya ce gazawar gwamnati na fara biyan sabon tsarin CONPCASS da CONTEDISS da kuma rashin kwararan matakai daga gwamnati ne suka tilasta shiga yajin aikin.

Gwamnatin Bauchi ta yiwa JAC barazana

Ahmed ya kuma zargi wakilan gwamnati da amfani da barazana domin tsoratar da shugabannin JAC da mambobinta a dukkanin manyan makarantun Bauchi.

Kara karanta wannan

"Shugabannin APC sun sace Naira tiriliyan 25?" PDP ta ba Tinubu shawarar abin yi

Saboda haka, JAC ta yanke shawarar shiga yajin aikin dindindin daga ranar Alhamis, 2 ga Janairu, 2025.

JAC ta bayyana cewa tana tausaya wa al’umma, musamman dalibai da iyayensu, kan duk tasirin da yajin aikin zai haifar ga karatunsu.

Malamai, ma'aikata sun gargadi gwamnati

Shugaban JAC ya ce a shirye kungiyar take ta koma bakin aiki idan gwamnati ta cika dukkanin bukatunsu.

Ahmed ya yi kira ga gwamnati da ta hanzarta magance bukatunsu domin kare lafiyar ilimi a jihar Bauchi.

Kungiyar JAC ta tabbatar wa jama’a cewa yajin aikin ba zai kare ba sai an cimma bukatun da suka gabatar wa gwamnati.

Malaman firamare sun shiga yajin aiki

A wani labarin na daban, mun ruwaito cewa rike hakkokin ma'aikata a babban birnin tarayya Abuja ya jawo malaman firamare sun tsunduma yajin aiki.

Shugaban kungiyar malamai a birnin tarayya Abuja, Kwamared Ameh Baba ya shaidawa manema labarai cewa sun tsunduma yajin aikin ne saboda gwamnati ta ki sallamarsu.

Kwamared Baba ya kuma jaddadawa gwamnati cewa nan gaba kadan malaman sakandare ne za su shiga yajin aikin idan gwamnati ba ta sakar masu hakkokinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.