An Ware Biliyoyi domin yin Hidima ga Akpabio, Barau da Sauran Shugabannin Majalisa

An Ware Biliyoyi domin yin Hidima ga Akpabio, Barau da Sauran Shugabannin Majalisa

  • An ware Naira biliyan 10 a cikin cikaton kasafin kudin 2024 domin hayar gidaje da kayan daki ga shugabannin majalisar kasa
  • Ware makudan kudin ya zo ne yayin da ‘yan Najeriya ke fuskantar matsananciyar wahala sakamakon tsare tsaren gwamnati
  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya sha suka kan lamarin, inda ake zargin yana amfani da shi da wata manufa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bincike ya nuna cewa shugabannin majalisa da mataimakansu sun samu Naira biliyan 10 domin hayar gidaje da kayan daki.

Hakan na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki, inda da dama suka rasa rayukansu yayin kokarin samun abinci kyauta a wasu wuraren.

Kara karanta wannan

2025: An gano yadda filin saukar jirgin Tinubu zai lakume N4bn ana kukan ba kudi

Majalisa
An ware N10bn ga shugabannin majalisa. Hoto: Nigerian Senate|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Binciken Premium Times ya nuna cewa kudin na cikin karin kasafin kudin 2024 da Bola Tinubu ya gabatar ga majalisa a watan Satumba, wanda aka amince da shi cikin kwanaki biyar kacal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ware N10bn ga shugabannin majalisa

Daily Trust ta wallafa cewa an sanya N10bn na hayar gidaje da kayan daki ga shugabannin majalisa cikin kasafin Naira biliyan 288 na Abuja.

Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda ake fama da wahala a kasar, yayin da gwamnatoci ke kiran jama’a su yi hakuri da tsauraran matakan tattalin arziki.

A cewar masana tattalin arziki, wannan kashe-kashen gwamnatin yana nuna rashin daidaito, musamman ganin yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsananciyar yunwa da rashin kudi.

Kashe kashen kudin da gwamnati ta yi

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sha yin irin wannan kashe-kashen kudi na alfarma, ciki har da Naira biliyan 21 da aka ware wajen gina katafaren gidan mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi zarra, ya gabatar da sama da Naira tiriliyan 1 a kasafin 2025

Bugu da ƙari, an zargi gwamnatin yanzu da kashe makudan kudi kan jirgin shugaban kasa na Dala miliyan 100 da sauran kayan alatu ga ‘yan majalisa.

A wannan karon, Sanata Godswill Akpabio, Barau Jibrin, Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu ne za su shiga cikin alheri da Naira biliyan 10 da aka ware.

Dattawan Rivers sun ja kunnen Wike

A wani rahoton, kun ji cewa dattawan jihar Rivers sun ja kunnen ministan Abuja kan kalamai da ya yi a kan tsohon gwamna Peter Odili.

Legit ta wallafa cewa dattawan jihar sun ce dole Nyesom Wike ya ba Peter Odili hakuri idan yana so a cigaba da ganin mutuncinsa a Rivers.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng