"Shugabannin APC Sun Sace Naira Tiriliyan 25?" PDP Ta ba Tinubu Shawarar Abin Yi
- PDP ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gudanar da bincike kan Naira trillion 25 da aka ce shugabannin APC sun sace
- PDP ta bukaci Shugaba Tinubu da ya magance kalubalen tsaro, abinci da man fetur don rage radadin da 'yan Najeriya ke fuskanta
- Jam'iyyar ta kuma yi kira ga shugaban kasar da ya yi bayanin inda aka kai biliyoyin Naira da aka samu daga janye tallafin man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam'iyyar PDP ta yi kira ga Bola Tinubu da ya gudanar da bincike tare da dawo da Naira trillion 25 da aka ce shugabannin APC sun sace.
Kiran yana kunshe a sanarwar sabuwar shekara da sakataren yada labaran PDP, Debo Ologuagba, ya sanyawa hannu.
A sanarwar da ta fitar ta shafinta na X, PDP ta bukaci Tinubu ya magance kalubalen tsaro, abinci da samar da man fetur don rage radadin da 'yan Najeriya ke fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da PDP ke so Bola Tinubu ya yi a 2025
Sanarwar ta ce:
“Muna fatan Tinubu ba zai yi jawabin da zai samar da matakan na rage farashin man fetur, magance matsalar yunwa da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kasar nan."
Jam'iyyar ta ce akwai bukatar shugaba Tinubu ya magance cin hanci, zamba da kashe kudin jama'a wajen jin dadin shugabannin APC.
PDP ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya bayyana yadda gwamnati ta yi da miliyoyin Naira da aka samu daga cire tallafin man fetur.
Jam'iyyar PDP ta nemi Tinubu ya binciki APC
PDP ta kuma bukaci shugaban ya bayyana matsayin gwamnatin sa kan yaki da cin hanci ta hanyar bincike da dawo da kudaden da shugabannin APC suka sace.
"Ya kamata mai girma shugaban kasa ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da kwato sama da Naira tiriliyan 25 da aka ce shugabannin APC da jami’an gwamnati sun sace."
- A cewar sanarwar.
Jam'iyyar ta ce shugabannin APC sun ci gaba da jin dadin rayuwar alatu yayin da talakawan Najeriya ke cikin yunwa da rashin tsaro.
PDP ta gargadi APC da ka da ta ci gaba da irin wannan hali a shekarar 2025, domin hakan zai kara jawo fushin 'yan Najeriya a kanta.
Filin saukar jirgin Tinubu zai lakume N4bn
A wani labarin, mun ruwaito cewa ma'aikatar ayyuka ta tarayya ta shirya ginawa shugaban kasa Bola Tinubu filin saukar jirginsa mai saukar angulu a Legas.
Aikin gina filin jirgin wanda zai lakume Naira biliyan hudu ya kuma hada da gina karamar tashar jirgin ruwa na shugaban kasar, duk dai a birnin na Ikko.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng