"Ba Mu Son Wa'azinku": Sanusi II Ya Fadawa Kasashen Yamma Abin da Arewa Ke Bukata
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya bukaci kasashen Yamma da su fifita ci gaban Arewa da samar da kayayyakin more rayuwa
- A wani jawabi a garin Jos, Sanusi II ya ce Arewa tana bukatar masu zuba jari a noma, ilimi da kiwon lafiya ba wai wa’azi ba
- Sarkin ya bayar da misalin karfin addini a Arewa kan yadda Kiristoci suka taimaka masa lokacin da aka tilasta masa barin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga kasashen Yamma da su mai da hankali kan ci gaban Arewacin Najeriya.
Khalifa Sanusi II ya bukaci kasashen Yamma da su fifita gina asibitoci, makarantu da masana'antu maimakon yada addini a Arewa.
Zuwan Nyass: An shirya taro a Jos
Sarkin ya yi wannan kira ne yayin gabatar da jawabi a bikin tunawa da ziyarar Sheikh Ibrahim Nyass a Jos shekaru 50 da suka wuce, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nyass, wanda ya kasance ginshikin darikar Tijjaniyya daga Senegal, ya kai ziyarar farko Jos ne a lokacin da Janar Yakubu Gowon ke shugabantar Najeriya.
An ce Da' Iratu Ahlus Sa'adah ta jihar Filato ta shirya wannan taron ne da nufin karfafa zaman lafiya da jituwa tsakanin addinai a yankin.
"Abin da Arewa ke bukata" - Sanusi II
Mai martaba sarkin Kano ya ce:
“Idan kun je Roma, Saudiyya ko Iran, kada ku je can don kawo addini. Muna da addini. Ku ce su zo su zuba jari a harkar noma."
Ya kuma kara da cewa:
“Idan har suna son Arewa, su kawo mana fasahar zamani, su gina mana asibitoci da makarantu. Kada su yada kiyayya ko gaba a tsakanin addinai."
Sarki Sanusi II ya ce ya dade da yin abokai Musulmi da Kiristoci kuma ko Lokacin da aka tilasta masa barin Kano, Kiristoci ne suka ba shi jirgin da ya hau.
Sanusi II ya fadi hadarin da Arewa ke ciki
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce rashin ci gaba ya jefa yankin Arewa cikin wahala, musamman a fannoni kamar ilimi da noma.
Sanusi II ya bukaci shugabanni da masu ruwa da tsaki da su zuba jari a ilimi da noma domin inganta rayuwar al'umma da ci gaban yankin Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng