Yanzu-Yanzu: Tsohon sarkin Kano Sanusi II ya bar Awe, jihar Nasarawa

Yanzu-Yanzu: Tsohon sarkin Kano Sanusi II ya bar Awe, jihar Nasarawa

Tubabben sarki, Malam Muhammadu Sanusi ya bar garin Awe da ke jihar Nasarawa. Ya bar garin ne tare da Malam Nasiru El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna a cikin mota daya.

Gwamnan na jihar Kaduna ya ziyarci tsohon sarkin bayan ya masa tayin wasu mukamai biyu a jiharsa kuma ya amsa.

Mukaman sun hada da shugaban gudanarwa na jami'ar jihar Kaduna wato KASU da kuma cibiyar saka saka hannun jari na Kaduna, KADIPA.

Yanzu-Yanzu: Mai martaba Sanusi II ya bar Awe, jihar Nasarawa

Yanzu-Yanzu: Mai martaba Sanusi II ya bar Awe, jihar Nasarawa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Mahaifiyar tubabben Sarki Sanusi II ta kai masa ziyara a Nasarawa (Bidiyo)

A wani rahoto na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya ce Muhammadu Sanusi II , tuɓaɓɓen Sarkin Kano yana da 'yancin tafiya ko wane gari har da Kano.

Bayan cire shi daga sarauta, akwai rahotanni da ke yaɗuwa na cewa ba shi da izinin shiga Kano na a ƙalla watanni uku.

Amma yayin amsa tambayoyin manema labarai a garin Awe a jihar Nassarawa, gwamnan na ya ce kotun babban birnin tarayya ta yanke hukuncin cewa Sanusi yana da ikon tafiya duk inda ya ke so.

El-Rufai ya ce, "Babban kotun ta yanke hukuncin cewa yana da 'yancin zuwa duk inda ya ke so, har da Kano amma ina tunanin yana son ya tafi Legas domin ya tarar da iyalansa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel